Da dumi-duminsa: Fargaba yayin da 'yan bindiga suka kona kauyen wani gwamna, sun kashe jami'an tsaronsa

Da dumi-duminsa: Fargaba yayin da 'yan bindiga suka kona kauyen wani gwamna, sun kashe jami'an tsaronsa

- Wasu mahara a Imo a ranar Asabar, 24 ga Afrilu, sun kai farmaki mahaifar Gwamna Hope Uzodinma

- ‘Yan bindigar sun kuma kona dukiya mai yawa, ciki har da motoci a Omuma a karamar hukumar Oru ta Gabas

- Hakanan wani jami’in gwamnati ya tabbatar da cewa an kashe wasu jami’an tsaro biyu da ke aiki a gidan gwamnan a wani artabu da ya biyo baya

Wasu gungun ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kona kauyen Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo, Omuma a karamar hukumar Oru ta Gabas, a ranar Asabar, 24 ga Afrilu, sun kuma yi nasarar kashe wani jami’in tsaro.

Wata majiya da ta zanta da jaridar Punch ta ce maharan a yayin artabu da jami'an tsaro, sun harbe biyu daga cikinsu, sannan ta kara da cewa wutar ta lalata ababen hawan a kauyen.

KU KARANTA KUMA: Gwamna El-Rufai ya samar da mafita ga hare-haren 'yan fashi a makarantu a Kaduna

Da dumi-duminsa: Fargaba yayin da 'yan bindiga suka kona kauyen wani gwamna, sun kashe jami'an tsaronsa
Da dumi-duminsa: Fargaba yayin da 'yan bindiga suka kona kauyen wani gwamna, sun kashe jami'an tsaronsa Hoto: @HopeUzodinma
Asali: Facebook

Kwamishinan yada labarai da dabaru, Declan Emelumba ya tabbatar da mummunan lamarin.

“Da gaske ne, amma har yanzu babu cikakken bayani. Ba gaskiya bane cewa jami’an tsaro da yawa sun rasa rayukansu.

"Kimanin jami’an tsaro biyu da ke bakin aiki a gidan gwamnan sun mutu. Jami'in NSCDC na daga cikin jami'an tsaron da suka rasa rayukansu yayin harin."

KU KARANTA KUMA: Jami'ar Greenfield: Daga karshe sunaye da hotunan ɗaliban da aka kashe sun bayyana

A wani labari na daban, rundunar sojoji sun kulle sansanin su dake Zagzaga yankin Munya, jihar Neja bayan yan bindiga sun sake kai wani sabon hari yankin.

Hakanan kuma sojojin sun ƙaddamar da sabon bincike tare da goyon bayan matasan yankin bisa bacewar wani soja a lokacin harin.

Wannan ya biyo bayan wani hari da yan bindiga su kimanin 60 suka kai sansanin sojojin ranar Laraba, inda suka yi musayar wuta a tsakaninsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel