Yan bindiga sun tilasta ma sojoji kulle sansaninsu, Sun yi awon gaba da mutane 15 a wani sabon hari a Neja

Yan bindiga sun tilasta ma sojoji kulle sansaninsu, Sun yi awon gaba da mutane 15 a wani sabon hari a Neja

- Sojoji sun kulle sansanin su na ƙauyen Zagzaga a jihar Neja biyo bayan wasu sabbin hare-hare da yan bindiga suka sake kaiwa yankin

- Sakataren gwamnatin jihar ta Neja yace an kulle sansanin ne saboda dabarar yaƙi kuma na wani ɗan lokaci ne

- A kwanakin baya ne dai yan bindiga suka kai hari a sansanin sojojin dake kauyen Zagzaga, inda suka yi musayar wuta a tsakaninsu

Rundunar sojoji sun kulle sansanin su dake Zagzaga yankin Munya, jihar Neja bayan yan bindiga sun sake kai wani sabon hari yankin.

Hakanan kuma sojojin sun ƙaddamar da sabon bincike tare da goyon bayan matasan yankin bisa bacewar wani soja a lokacin harin.

KARANTA ANAN: Dalilin da yasa Pantami ya tsallake binciken DSS duk da mun gano kalamansa, Tsohon Darakta yayi bayani

Wannan ya biyo bayan wani hari da yan bindiga su kimanin 60 suka kai sansanin sojojin ranar Laraba, inda suka yi musayar wuta a tsakaninsu.

Yan bindigar sun sami munanan raunuka, amma babu wani soja da ya samu rauni in banda guda ɗaya da ya ɓata kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Sojojin sun fita daga yankin a abinda sakataren gwamnatin jihar, Ibrahim Matene, ya kira da 'Salon yaƙi'.

Awanni kaɗan da fitar sojojin, yan bindigar suka sake kai sabbin hare-hare a wasu kauyukan dake yankin, wata majiya ta faɗama Dailytrust.

Yan bindiga sun tilasta ma sojoji kulle sansaninsu, Sun yi awon gaba da mutane 15 a wani sabon hari a Neja
Yan bindiga sun tilasta ma sojoji kulle sansaninsu, Sun yi awon gaba da mutane 15 a wani sabon hari a Neja Hoto: independent.ng
Asali: UGC

Rahotanni sun tabbatar da sun sace mutane 15 a harin da suka kai da daddare, suka tilasta ma mazauna yankin guduwa zuwa ƙauyukan dake kusa dasu.

Mutanen kauyukan da harin ya shafa duk sun canza wurin zama, sun bar matasa da wasu tsirarun mutane.

KARANTA ANAN: Bincike: Mafi yawancin Gwamnonin dake kan madafun iko sun fito ne daga wannan jami'ar

Kauyukan da sabbin hare-haren suka shafa sune; Zagzaga, Zhani, Guni da kuma Maraban Daudu.

Wata majiya tace, yan bindigar sun sace mutane 15 a kauyen Boddo da sanyin safiyar ranar Alhamis.

Lokacin da aka tuntuɓi sakataren gwamnatin jihar kan sabbin hare-haren, yace an kulle sansanin sojojin ne na wani ɗan lokaci saboda dabarar yaƙi.

Ya kuma ƙara da cewa sojojin sun kasance a wannan yankin na tsawon shekaru biyar da suka gabata saboda matsalolin dake yawan faruwa.

Yace ƙauyen Zagzaga da wasu ƙauyuka dake kusa dashi sun kasance hanyar shige da ficen yan bindiga kafin sojojin suzo su zauna a wajen.

A wani labarin kuma Yan Sanda sun damƙe mutane huɗu da zargin kashe wani Sabon ango kwana ƙaɗan kafin bikinsa

Mutanen sun yaudari angon zuwa wani daji inda suka kashe shi kuma suka nemi amaryarsa ta biya 12 miliyan kuɗin fansa.

Waɗanda ake zargin sun amsa laifinsu, inda suka bayyana duk yadda akayi har suka yaudare shi zuwa dajin da suka kashe shi a can.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262