Jam’iyyar APC Kaduna ta kafa tarihi a Najeriya, ta gudanar da jarrabawa ga masu neman kujerun ciyamomi
- Zama shugaban karamar hukuma a Kaduna a karkashin jam'iyyar APC ba wasa bane a yanzu
- Jam’iyya mai mulki ta gudanar da gwaje-gwaje masu wahala ga dukkan masu neman takararta a ranar Laraba, 21 ga Afrilu
- Manufar jarabawar ya kasance don gujewa zabar mutane da ke da matsala da takardunsu wanda hakan ka iya jefa jam’iyyar ga shiga kararrakin bayan zabe
A wani yunkuri na kaucewa zaben mutanen da ke da guntun kashi a tarihinsu, jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a Kaduna ta gudanar da jerin jarabawa ga dukkan masu neman kujerun shugabanci na ciyaman.
A cewar wani rahoto da jaridar The Nation ta fitar, jarabawar wacce ta kasance a rubuce da ta baki ta dauki tsawon awanni a ranar Laraba, 21 ga Afrilu.
KU KARANTA KUMA: An kashe mutum 45, da dama sun bata yayinda yan bindiga suka kai mamaya garuruwan Zamfara 6
An tattaro cewa an bukaci masu neman takarar (sama da mutum 100) su yi kwafin takardun makarantarsu sannan kuma su gabatar da su ga kwamitin da ya kunshi furofesoshi, lauyoyi, da likitoci a fannoni daban-daban na boko.
Daya daga cikin ‘yan takarar da ya zanta da manema labarai a wurin jarabawar, Stonehedge Hotel a jihar, ya ce sai da suka rubuta labaran rayuwarsu, makarantun da suka halarta, gami da kwarewar aiki.
KU KARANTA KUMA: Rikicin PDP: Bangaren Kwankwaso sun dau fansa, an dakatar da Sanata Gwarzo
A wani labari na daban, mutuwar wasu mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) biyar a jihar Oyo ya jefa jam’iyyar cikin alhini.
A cewar Jaridar The Sun, Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya bayyana cewa mambobin jam’iyyar da suka mutu an zabe su kansiloli ne a karkashin inuwar jam’iyyar.
Teslim Folarin, wani tsohon dan majalisar dattijai ya jajantawa majalisar dokokin jihar Oyo kan wannan abun bakin cikin.
Asali: Legit.ng