Sufetan Yan sanda na ƙasa ya roƙi a ƙaro ma hukumarsa kuɗi domin daƙile dukkan matsalolin tsaro

Sufetan Yan sanda na ƙasa ya roƙi a ƙaro ma hukumarsa kuɗi domin daƙile dukkan matsalolin tsaro

- Sufetan yan sanda na riƙo, Usman Alƙali Baba, ya buƙaci a ƙara ma hukumar yan sanda kuɗi domin su ƙara ƙaimi wajen sauke nauyin dake kansu na yaki da laifuffuka

- IGP ya bayyana haka ne a wata ziyara ta musamman da ya kaima kakakin majalisar wakilai domin nuna godiyarsa bisa ɗumbin goyon bayan da majalisa ke baiwa hukumarsa

- Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ya nuna jin daɗinsa da ziyarar kuma yace yakamata Najeriya ta dawo da martabar yan sanda

Sufetan yan sanda na riƙo (IGP), Usman Alƙali Baba, ya ƙara yin kira da a ƙaro ma hukumarsa kuɗi domin bata damar sauke nauyin dake kanta na daƙile ƙaruwar rashin tsaro a cikin ƙasa.

KARANTA ANAN: Bamu tattauna a kan zargin da ake ma sheikh Pantami ba a wajen taron FEC, Inji Lai Muhammed

Yayi wannan kira ne a lokacin da ya ziyarci kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, ranar Laraba kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

IGP ɗin yace ya kawo wannan ziyara ne domin yin godiya ga Gbajabiamila da sauran yan majalisu bisa goyon bayan da hukumar yan sanda ke samu daga yan majalisun.

Yace yayi matuƙar jin daɗin yadda yan majalisun basu ɗauki dogon lokaci ba wajen amincewa da kudirin hukumar na zamanantar da aikin ɗan sanda.

Ya kuma yi roƙon da a gaggauta amincewa da sauran kudirorin da suka shafi hukumar yan sanda waɗanda suka haɗa da kudirin ƙirƙiro hukumar kula da ayyukan yan sanda.

Baba yace jami'an yan sanda na aiki ne cikin rashin kuɗi, ya ƙara da cewa jami'an zasu fi dagewa idan yan majalisu suka goya musu baya suka sami ƙarin kuɗaɗe.

Sufetan Yan sanda na ƙasa ya roƙi a ƙaro ma hukumarsa kuɗi domin daƙile dukkan matsalolin tsaro
Sufetan Yan sanda na ƙasa ya roƙi a ƙaro ma hukumarsa kuɗi domin daƙile dukkan matsalolin tsaro Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Alkali baba yace:

"A ɓangaren kuɗin da ake turo mana, muna buƙatar goyon bayanku sosai domin bamu samun isassun kuɗi. Muna da baiwa ne kawai ta yin aiki idan aka kwatatanta da abinda muke samu."

KARANTA ANAN: Wata Mata ta mare ni a gaban mijinta bance komai ba, ɗan sandan da gwamnan Lagos ya karrama

A ɓangarensa, kakakin majalisar wakilai yace Najeriya na buƙatar yin aiki tuƙuru wajen dawo da martabar hukumar yan sanda.

Wanda a cewarsa hakan zai taimakama jami'an hukumar samun nasara kan ayyukan da aka ɗora musu na yaƙi da laifuffuka.

Yace: "Dan sanda ginshiƙi ne na tsaida doka, babban abinda yafi ɓuƙata daga jama'ar yankinsa shine girmamawa, wannan zai bashi damar yin aikinsa bisa doka."

"Aikin ɗan sanda na matuƙar buƙatar nazari, meyasa zakaga yan sanda sun fito kan hanya a rikirkice? Kayansu duk sunyi datti kuma sun saka takalmi silifa."

"Saboda haka ne mutane basu girmama su, basu jin wani abu dan sun gansu yayin da suka zo tsaida doka. A wasu ƙasashen, idan ɗan sanda yazo wuri, kayan aikin dake tare dashi kaɗai sun isa su hana faruwar laifi."

A wani labarin kuma Rundunar Yan sanda ta Kuɓutar da yara ƙanana 19 da wasu mata 6 da ake ƙoƙarin safararsu

Rundunar yan sanda reshen jihar Edo ta kuɓutar da mutane 26 a jihar waɗanda akayi kokarin safarar su.

Hukumar tace waɗanda ta kuɓutar ɗin sun haɗa da ƙananan yara 19, da kuma matashiya ɗaya, sai kuma iyaye mata su shida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262