Rikicin PDP: Bangaren Kwankwaso sun dau fansa, an dakatar da Sanata Gwarzo

Rikicin PDP: Bangaren Kwankwaso sun dau fansa, an dakatar da Sanata Gwarzo

- An yi baran-baran a zaben yankin Arewa maso yamma na shugabannin PDP

- Bayan haka aka dakatar da jagoran PDP a jihar, Sanata Rabiu Kwankwaso

- Yanzu kuma an dakatar da daya daga cikin yan takara a zaben

Rikicin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), reshen jihar Kano ya dau sabon salo ranar Laraba yayinda aka dakatar da Sanata Bello Hayatu Gwarzo, dan takaran kujeran mataimakin shugaban uwar jam'iyya.

Gwarzo wanda ya kasance dan bangaren tsohon minista Aminu Wali, ya samu takardar dakatarwa daga Shugabannin jam'iyyar PDP a gundumarsa.

A makon da ya gabata, bangaren Aminu Wali sun dakatad da tsohon gwamnan jihar, Rabiu Musa Kwankwaso, amma uwar jam'iyya tayi watsi da hakan.

An sanar da dakatad da Gwarzo ne a wasika mai ranar wata, 20 ga Afrilu wanda Sakataren PDP a gundumar, Idris Danbaba da shugaba Sanusi Ibrahim suka rattafa hannu.

A cewar wasikar da Daily Trust ta samu, an dakatad da Gwarzo ne bisa zargin yiwa jam'iyya zagon kasa.

KU KARANTA: Munanan hare-hare, kashe-kashe da garkuwa da mutane 5 da ya suka auku jiya Laraba

Rikicin PDP: Bangaren Kwankwaso sun dau fansa, an dakatar da Sanata Gwarzo
Rikicin PDP: Bangaren Kwankwaso sun dau fansa, an dakatar da Sanata Gwarzo Credit: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA NAN:Sai kun kara mana kudi zamu iya kawar da yan ta'adda, Shugaban Hafsan Soji Attahiru

Kimanin makonni 2 da suka gabata mun kawo muku rahoton cewa rikici ya barke yayin zaben shugabannin jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party PDP na shiyar Arewa maso yammacin Najeriya ranar Asabar.

Wasu mambobin jam'iyyar sun bayyana rashin gamsuwarsu da yadda akayi tsarin zaben kuma hakan ya sa suka fasa akwatunan zaben kuma suka rikirkita wajen da ake zaben.

An gudanar da taron zaben ne a unguwar Rigachikun ta jihar Kaduna.

Manyan masu takaran kujeran mataimakin shugaba na yankin Arewa maso yamma sune Sanata Bello Hayatudeen Gwarzo, da kuma wani na hannun daman tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.

Asali: Legit.ng

Online view pixel