Jerin sunaye: Babban ibtila’i ya afkawa APC yayin da shugabannin jam'iyyar 5 suka Mutu Ba zato ba tsammani

Jerin sunaye: Babban ibtila’i ya afkawa APC yayin da shugabannin jam'iyyar 5 suka Mutu Ba zato ba tsammani

- Ana jimamin mutuwar Kansilolin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) biyar a jihar Oyo

- Teslim Folarin, tsohon dan majalisar dattijai ya jajantawa majalisar dokokin jihar Oyo kan wannan rashi da tayi

- Sai dai kuma ba a bayyana abin da ya yi sanadin mutuwar kansilolin ba

Mutuwar wasu mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) biyar a jihar Oyo ya jefa jam’iyyar cikin alhini.

A cewar Jaridar The Sun, Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ya bayyana cewa mambobin jam’iyyar da suka mutu an zabe su kansiloli ne a karkashin inuwar jam’iyyar.

Teslim Folarin, wani tsohon dan majalisar dattijai ya jajantawa majalisar dokokin jihar Oyo kan wannan abun bakin cikin.

Jerin sunaye: Babban ibtila’i ya afkawa APC yayin da shugabannin jam'iyyar 5 suka Mutu Ba zato ba tsammani
Jerin sunaye: Babban ibtila’i ya afkawa APC yayin da shugabannin jam'iyyar 5 suka Mutu Ba zato ba tsammani Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Duk da huro masa wuta da akai ya sauka a kan muƙaminsa, Sheikh Pantami ya halarci taron majalisar zartarwa

Folarin ya ce:

Na yi matukar kaduwa da bakin ciki da jin wannan babban rashi na wasu zababbun kansiloli a karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Oyo.

“Zuciyata ta tausayawa majalisar, iyalan APC, mazabun da suka wakilta da kuma iyalan da suka bari.''

A cewar Peoples Gazette, tsohon dan majalisar ya ce za a tuna da marigayi ‘yan siyasar saboda gudummawar da suka bayar don daukaka talakawa.

Ya yi addu'a ga Allah Madaukakin Sarki da ya hutar da rayukansu cikin kwanciyar hankali kuma ya ba dukkansu ƙarfin zuciyar daukar wannan rashi.

Dan siyasar bai bayyana abin da ya yi sanadin mutuwar kansilolin ba.

Daga cikin mamatan akwai:

1. Honarabul Rukayat Adejumobi daga Karamar Hukumar Itesiwaju

2. Honorabul Oluyemi Muhammad daga yankin cigaban karamar hukumar Ibadan ta kudu (LCDA).

3. Honarabul Oluwole Adesokan daga Akinyele,

4. Honourable Asimiyu Ajayi daga Ido

5. Honorabul Moruf Agbedo daga Egbeda

KU KARANTA KUMA: Najeriya na tarwatsewa farfesoshi na iya komawa aiki a gidan Burodi, Lai Mohammed

A wani labari na daban, mun ji cewa gobara ta tashi a zauren majalisar dokokin jihar Katsina.

Lamarin na zuwa ne kwanaki 30 bayan faruwar irin haka a babbar kasuwar Katsina inda aka yi asarar kayayyaki na biliyoyin nairori.

A cewar wani ganau, gamayyar jami’an kashe gobara da na tsaro da ke ofishin majalisar dokokin ne suka kashe wutar, sannan cewa ba a rasa rai ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel