Wata sabuwa: Kabilar Yaohnanen masu bautawa mijin Sarauniyar Ingila
- Yarima Philip ya mutu amma mutanen wata kabila a tsibirin Vanuata sunyi imanin cewa zai dawo tsibirin su
- Kabilar Yaohnanen suna bautar Yariman a matsayin Allansu kuma sunyi imanin cewa zai kawo zaman lafiya da jituwa a duniya
- A cewar kabilun, Doya da suke shukawa a kowace shekara tana kiyaye ruhin Yarima Philip ya kasance rayayye
Mutanen kabilar Yaohnanen da ke tsibirin Vanuata wadanda ke bauta wa Yarima Philip a matsayin allansu sun ce sun yi imanin cewa ruhinsa zai dawo gida garesu a tsibirinsu.
A cewar mutanen, marigayi Duke na Edinburgh zai kawo zaman lafiya da jituwa a duniya, Daily Mail ta ruwaito.
Wani daga cikin 'yan kabilar ya ce duk wani farin ciki daga gare shi yake, yayin da wani ya ce yana matukar kaunarsa kuma yana addu'ar cewa rayuwarsa ta hadu da ta Yarima Philip.
Wani mutum ya ce: "Shi ruhi ne kuma dan allahnmu ne. Kowa ya yi imani da shi kuma sunansa Prince Philip."
KU KARANTA: ‘Yan bindiga sun sace wasu ma’aikatan gini guda uku a jihar Ondo
Mutanen kabilar sun kasance suna rike da annabcin da ke cewa lokacin da aikin Yarima Philip ya kare a Ingila, zai dawo gida garesu.
Wani dan kabilar ya ce suna shuka sabbin Doya a kowace shekara wanda ke ba ruhin Yarima Philip rai.
Ya ce: "Kowace shekara muna shuka sabbin Doyoyi wadanda suke fitar da sabbin saiwowin da ke kiyaye ruhin Yarima Philip.
"Wannan Doyar tana yaduwa zuwa na gaba, wanda kuma ke fitar da sabbin doya. Ma'ana cewa ba zai taba mutuwa ba saboda ruhin Doya yana dawwama."
KU KARANTA: Manhajar albashin jihar Bauchi ta lalace, an dakatar da albashin wasu ma'aikata
A wani labadarin daban, Majalisar dattijai na nazarin kudirin dokar da ke neman samar da rumbun adana bayanan shanu a duk fadin kasar, The Cable ta ruwaito.
Kudurin dokar da za a samar a Hukumar Kula da Kiwo ta Kasa ta zarce karatu na biyu a zaman majalisar na ranar Talata.
Dangane da dokar, wacce Muhammad Enagi daga Neja ta kudu ya bijiro da ita, hukumar za ta kasance mai kula da ganowa, bincikowa da kuma yin rajistar dabbobi kamar shanu da awaki da sauran abubuwa, da tunanin hakan zai hana satar shanu.
Asali: Legit.ng