Gobara ta tashi a zauren majalisar dokokin jihar Katsina
- Ya zama dole gwamnatin jihar Katsina ta kara kashe kudade domin gyara majalisar dokokin jihar
- Wannan ya biyo bayan wata gobara da ta lakume zauren majalisar
- An danganta faruwar lamarin da barin kayan lantarki da aka yi a kunne
Rahoto daga kafar watsa labarai ta Channels TV ta fitar ya nuna cewa gobara ta tashi a zauren majalisar dokokin jihar Katsina.
Lamarin na zuwa ne kwanaki 30 bayan faruwar irin haka a babbar kasuwar Katsina inda aka yi asarar kayayyaki na biliyoyin nairori.
A cewar wani ganau, gamayyar jami’an kashe gobara da na tsaro da ke ofishin majalisar dokokin ne suka kashe wutar, sannan cewa ba a rasa rai ba.
KU KARANTA KUMA: Jiya ba yau ba: Bullar rasiɗin sayen mota ƙirar 'Beetle' kan Naira 3,908 ya jawo cece kuce
A halin yanzu, Mataimakin Babban Mai tsawatarwa na majalisar kuma mamba mai wakiltar mazabar Kankia, Salisu Rimaye ya ce babu wanda zai iya cewa ga ainihin abin da ya haddasa lamarin.
Ya ce Majalisar ta samu labarin faruwar lamarin ne lokacin da magatakardar majalisar ya umurci Sajan na bangaren da ya je ya tsabtace zauren majalisar.
Ya bayyana cewa Sajan din ya bude zauren sannan kuma ya gano lamarin.
Ya ci gaba da bayyana cewa wata kungiyar ma'aikatan wutar lantarki a Majalisar ta fara aiwatar da wani aiki na musamman domin sanin abunda ya haddasa shi amma, ya danganta hakan da kayan lantarki musamman na'urar sanyaya daki da aka bari a kunne.
Wutar ta fara daidai bayan kujerar Shugaban Majalisar inda kujerar kakakin gaba daya ta kone kurmus.
Sauran wuraren da lamarin ya shafa su ne dakin saukar yan jarida da baki tare da wasu kujerun wasu mambobin majalisar.
Gwamnan jihar Aminu Masari ya kai ziyara domin duba abin da ya faru inda ya tausaya wa Mataimakin Babban Mai tsawatarwa da sauran manyan jami'an majalisar.
KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun sake kai hari wani sansanin sojoji a jihar Neja
A halin da ake ciki, rahotanni sun ce majalisar tana yajin aiki a lokacin da lamarin ya faru saboda neman ikon cin gashin kai daga bangaren zartarwa.
A kwanan nan ne gwamnatin jihar Katsina ta gyara zauren majalisar.
A gefe guda, majalisar dattawa a ranar Laraba ta amincewa gwamnatin tarayya ta karbi sabon bashin $1.5bn da €995m daga kasashen waje.
A lissafin da muka buga, wannan kudi ya kama N1.1tr a kudin Najeriya.
Sanatocin sun amince gwamnati ta karbi wannan bashi ne bayan kwamitin basussuka na majalisa ta gabatar da rahotonta kan shirin karban bashin gwamnatin tarayya.
Asali: Legit.ng