Manhajar albashin jihar Bauchi ta lalace, an dakatar da albashin wasu ma'aikata

Manhajar albashin jihar Bauchi ta lalace, an dakatar da albashin wasu ma'aikata

- Gwamnatin jihar Bauchi ta dakatar da albashin wasu ma'aikata da take zargin na bogi ne

- Jihar ta bayyana cewa, za ta bar hukumomi da ma'aikatun jihar su tantance ma'aikatansu

- Hakazalika, gwamnatin ta koka kan yadda aka yi kutse cikin manhajar biyan albashin jihar

Sakataren Gwamnatin Jihar Bauchi, Alhaji Mohammed Baba, ya ce gwamnati ta dakatar da albashi na wani lokaci na wasu da ake zargin ma’aikatan bogi 715, jaridar Punch ta ruwaito.

Baba ya fadi haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan sakamakon taron ranar Laraba na Majalisar Zartaswar Jiha a gidan Gwamnati da ke Bauchi.

“Muna da jerin sunayensu kuma an ba da dalilin dakatar da kowane albashi balo-balo.

“Abin da gwamnati ke son yi shi ne ta nemi kwamishinonin da ke kula da ma’aikatu daban-daban da kuma sassa da hukumomi su yi nasu jerin sunayen sannan su koma ga wadancan mutanen, su zauna su tantance su.

KU KARANTA: ‘Yan bindiga sun sace wasu ma’aikatan gini guda uku a jihar Ondo

Manhajar albashin jihar Bauchi ta lalace, an dakatar da albashin wasu ma'aikata
Manhajar albashin jihar Bauchi ta lalace, an dakatar da albashin wasu ma'aikata Hoto: theguardian.ng
Asali: UGC

“Yana da kyau idan abu ne da za a iya warware shi amma idan ba zai yiwu ba, to, wannan ya tabbata shine irin abin da muke fada game da ma’aikatan bogi a cikin tsarin.

“Tabbas, gwamnati ba za ta iya ci gaba da biyan mutanen da ba su cancanci a biya su ba,” in ji Baba.

Ya ce gwamnati ta gano cewa tsarin da ake amfani da shi wajen biyan albashi a jihar ya lalace.

A cewarsa, makasudin gabatar da taron shi ne don fadan irin ci gaban da gwamnati ke samu wajen magance kalubalen albashi a jihar.

”Manufar kwamitin da aka kafa kimanin makonni hudu da suka gabata shi ne a samu albashi, inda kuma ba a sauya jihar ba.

“Tun lokacin da muka zo, akwai rufa-rufa da koke-koken cewa akwai ma’aikatan bogi da yawa a cikin tsarin biyan albashi na jihar, manufar ita ce a magance wannan matsalar kwata-kwata.

"Akwai hadin baki tsakanin wadanda suka ci gajiya da kuma ma'aikata da ya jawo har aka bude manhajar da muke amfani da ita don yin magudi da yawa, saboda haka, ba za mu iya dogaro da ita ba," in ji Baba.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun sake sace daliban jami'a a Kaduna

A wani labarin, Lai Mohammed, Ministan yada labarai da al’adu, ya ce yana da kyau manyan Najeriya su fahinci ci gaba da kasancewar Najeriya kasa daya, TheCable ta ruwaito.

Mohammed ya bayyana hakan ne a ranar Laraba lokacin da yake gabatarwa a wani shirin hira da jaridar NAN, NAN Forum.

Ministan ya zargi manyan mutane da ruruta wutar wargajewar kasar, kuma ya yi gargadin cewa za su dauki mafi girman munin sakamako idan Najeriya ta rabu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel