Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun sake sace daliban jami'a a Kaduna

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun sake sace daliban jami'a a Kaduna

- 'Yan bindiga sun sake kai hari wata jami'a a jihar Kaduna in da suka yi awon gaba da dalibai

- A kokarin kutsawa makarantar 'yan bindigan sun harbi mai gadi da aka ruwaito ya mutu

- Wannan shine karo na uku kenan da 'yan bindiga ke kawo hari makarantu a fadin jihar Kaduna

Wasu ‘yan bindiga sun sace daliban da ba a san adadin su ba daga Jami’ar Green Field da ke jihar Kaduna.

Jaridar TheCable ta fahimci cewa 'yan bindigan sun farma makarantar ne da tsakar daren Talata.

An ce sun bude wuta ne don tsoratar da mazauna yankin kafin su sace wasu daliban.

Jami’ar mai zaman kanta tana kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuka a karamar hukumar Chikun, daya daga cikin wuraren da ‘yan bindiga suke a Kaduna.

Ba a samu jin ta bakin Samuel Aruwan ba, kwamishanan tsaro da lamuran cikin gida na jihar Kaduna.

KU KARANTA: Majalisar Dattawa na duba yiyuwar hanyar sanin yawan shanu da awakai a Najeriya

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun sake sace daliban jami'a a Kaduna
Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun sake sace daliban jami'a a Kaduna Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Lamarin na baya-bayan nan ya zama hari na uku da aka kaiwa makarantu a jihar a shekarar 2021.

An tuntubi Mohammed Jalige, kakakin ‘yan sanda na Kaduna, amma har yanzu ba a samu amsa ba.

Makonni biyar da suka gabata, ‘yan bindiga sun afka wa makarantar firamare ta UBE da ke Rama a karamar hukumar Birnin-Gwari, kwanaki bayan makamancin wannan harin.

A baya sun kai hari kan Kwalejin Noma da Ilimin Gandun Daji ta tarayya a karamar hukumar Igabi, inda suka yi awon gaba da dalibai 39, 10 daga cikinsu sun kubuta.

Iyayen daliban 29 wadanda ke hannun har yanzu, sun ci gaba da gudanar da zanga-zanga, suna neman gwamnatin jihar da ta tattauna da ‘yan bindigan don ganin an sako yaransu.

Sun kuma yi barazanar tunkarar 'yan bindigan bayan ya bayyana cewa gwamnatin jihar ba za ta tattauna da maharan ba.

Nasir el-Rufai, gwamnan Kaduna, ya dage cewa ba zai dauki wannan matakin ba, yana mai gargadin illar hakan.

KU KARANTA: Majalisar Dattawa na duba yiyuwar hanyar sanin yawan shanu da awakai a Najeriya

A wani labarin, Karamin ministan Buhari a hukumar ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba ya koka kan yadda lamarin yake kara yawaita.

Ya bayyana cewa, gwamnati na jin zafin yawaitar satan, ya kuma bayyana cewa shi da kansa ya na 'ya'ya a makarantar gwamnati.

Ministan ya bayyana haka yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels a jiya Talata 20 ga watan Afrilu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel