Duk da huro masa wuta da akai ya sauka a kan muƙaminsa, Sheikh Pantami ya halarci taron majalisar zartarwa
- Duk da matsin lambar da yake sha na ya sauka daga muƙaminsa, Sheikh Pantami ya halarci taron majalisar zartarwa na yau Laraba
- Taron wanda shugaba Buhari ke jagoranta a karon farko tun bayan dawowarsa daga Landan inda ya kwashe makwanni biyu wajen duba lafiyarsa
- Pantami yayi watsi da dukkan kiran da ake masa na ya aje aikinsa, ya bayyana hakan da cewa siyasa ce kawai
Ministan sadarwa da tattalin arziƙin zamani, Dr. Isa Pantami, ya halarci taron majalisar zartarwa na yau Laraba wanda shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ke jagoranta.
Wannan na zuwa ne biyo bayan kiraye-kirayen da ake ma ministan na ya ajiye muƙaminsa saboda maganganun da yayi a baya kan yan ta'addan Taliban da Alƙa'ida.
KARANTA ANAN: Sheikh Pantami ya bayyana wata babbar Nasarar da gwamnatin tarayya ta samu a ɓangaren Fasahar Zamani
Amma Pantami yayi watsi da kiraye-kirayen, inda ya halarci taron majalisar zartarwa wanda yake gudana a fadar shugaban ƙasa dake Abuja.
Taron dai shine karo na farko da shugaba Buhari ya jagoranta tun bayan dawowarsa daga Landan, inda ya shafe sama da makwanni biyu.
Wannan na ƙunshe ne a wani saƙo da ma'aikatar sadarwa da tattalin arzikin zamani ta fitar a shafinta na tuwita, ma'aikatar tace:
"Ministan sadarwa da tattalin arziƙin zamani, Dr. Isa Pantami na ɗaya daga cikin waɗanda suka halarci taron majalisar zartarwa wanda shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ke jagoranta, ta hanyar amfani da fasahar zamani (Virtually)"
Ma'aikatar ta kuma tura hotunan da suka nuna Minista Pantami, shugaba Buhari, da sauran yan majalisar zartarwa a wajen taron.
KARANTA ANAN: Wata Mata ta mare ni a gaban mijinta bance komai ba, ɗan sandan da gwamnan Lagos ya karrama
Ministan, wanda aka huro ma wuta kan kalaman da yayi a baya waɗanda suke nuni da goyon bayan wasu ƙungiyoyin yan ta'adda, yace ya canza wadannan maganganun da yayi.
Ya ce yanzun ya ƙara ilimi da gogewa amma duk da haka wasu yan Najeriya na cigaba da kiran ya ajiye muƙaminsa.
Wasu kuma na ganin bayanin da yayi ya gamsar, kuma ana buƙatar mutum mai ilmi da gogewa kamarsa a ofis ɗin ministan.
Sai dai duk da kiraye-kirayen da ake masa ya sauka a muƙamin nasa a dandalin sada zumunta na Tuwita, ministan bai sauka ba kuma shugaba Buhari bai sallameshi ba.
A wani labarin kuma Rundunar Yan sanda ta Kuɓutar da yara ƙanana 19 da wasu mata 6 da ake ƙoƙarin safararsu
Rundunar yan sanda reshen jihar Edo ta kuɓutar da mutane 26 a jihar waɗanda akayi kokarin safarar su.
Hukumar tace waɗanda ta kuɓutar ɗin sun haɗa da ƙananan yara 19, da kuma matashiya ɗaya, sai kuma iyaye mata su shida.
Asali: Legit.ng