'Yan sandan Najeriya 144 sun isa Somaliya domin tabbatar da tsaro
- An tura jaruman 'yan sandan Najeriya zuwa kasar Somaliya don tabbatar da zaman lafiya
- Sun isa kasar ta Somaliya ne don gudanar aikin tabbatar da bin doka da oda tare da takwarorinsu
- Sun kuma tabbatar da cewa, a shirye suke don fara aiki tukuru ba tare da bata lokaci ba a kasar
Tawagar 'yan sanda 144 daga Najeriya sun isa kasar Somaliya domin bunkasa ayyukan tabbatar da tsaro a kasar, in ji tawagar Tarayyar Afirka a ranar Lahadi. CGTN Africa ta ruwaito.
Mai kula da ayyukan ‘yan sanda na rundunar 'yan sanda Daniel Ali Gwambal ya ce za a tura jami’an ‘yan sanda 30 da za su yi aiki a karkashin AMISOM na tsawon shekara guda zuwa Beletweyne da ke cikin jihar HirShabelle.
Ya kuma bayyana cewa, sauran za su yi aiki a wurare daban-daban a Mogadishu, babban birnin kasar.
KU KARANTA: Firaministan Pakistan ya yi kira ga tsaurara hukunci kan masu batanci ga Annabi
Gwambal a cikin wata sanarwa da ya fitar a Mogadishu ya ce; "Sun zo nan ne domin cika wa'adin AMISOM game da goyon bayan aiki ga 'yan Somaliya da kuma jagorantar rundunar 'yan sanda ta Somaliya (SPF)."
"Akwai wasu takamaiman ayyuka wadanda ya kamata su yi yayin da suke nan, kamar yin sintiri a kai-a kai a wuraren binciken ababen hawa, aikin gadi da sauran ayyukan da suka shafi aikin dan sanda," in ji shi.
Gwambal ya ce jami’an za su yi aiki a kan samar da rakiya ga muhimman mutane da aiyukan kariya, horo da kuma taimakawa rundunar ta SPF a cikin tsarin tafiyar da tsarin jama’a.
Za kuma su gudanar da sintiri tare da takwarorinsu na Somaliya da kuma samar da muhimman wuraren gwamnati da manyan taruka.
Tawagar ta AU ta ce zuwan rundunar wani babban ci gaba ne ga kokarin bin doka da oda, domin za su yi aiki tare da takwarorinsu na Somaliya wajen tabbatar da ingantaccen tsaro a yankunan da aka kwato.
Kwamandan rundunar da aka tura, Samuel Ita, ya ce jami'ansa sun himmatu don fara gudanar da ayyukansu, don taimakawa ci gaban ayyukan da aka ba su.
KU KARANTA: Buhari ya nuna matukar damuwa kan yawaitar hatsarin tankuna a Najeriya
A wani labarin, Rundunar tsaro ta hadin gwiwa a karamar hukumar Shiroro da ke jihar Neja ta kashe 'yan bindiga shida a yayin wani samame na dakile harin da 'yan ta'addan suka kai a yankin Garkogo, The Nation ta ruwaito.
An ce 'yan bindigar sun kai hari a wasu kauyukan da ke kusa da Garkogo amma rundunar hadin gwiwar ta fatattake su.
Bayanai sun ce rundunar ta dauki matakin ne bayan wani labari da ta samu kan harin da aka kai kauyukan a safiyar ranar Asabar inda suka yi kwanto da ‘yan bindigan.
Asali: Legit.ng