Yanzu Yanzu: EFCC ta kama tsohon gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari

Yanzu Yanzu: EFCC ta kama tsohon gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari

- Hukumar EFCC a yanzu haka tana yi wa tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari tambayoyi kan wasu zarge-zargen cin hanci da rashawa

- An tattaro cewa an rike tsohon gwamnan a ofishin hukumar na Sakkwato na tsawon awanni takwas har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton a ranar Talata, 20 ga watan Afrilu

- Majiya ta ce an bayar da belin Yari amma bai iya cika sharuddan belin ba

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa yanzu haka tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, yana hannun hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC).

A cewar rahoton, jami'an EFCC na yi wa Yari wasu tambayoyi kan zarge-zargen cin hanci da rashawa.

KU KARANTA KUMA: Gwamnan Najeriya na shirye-shiryen barin kujerarsa, ya fice daga gidan gwamnati

Yanzu Yanzu: EFCC ta kama tsohon gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari
Yanzu Yanzu: EFCC ta kama tsohon gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari Hoto: @AbdulAzizAYari
Asali: Twitter

An ce an tsare tsohon gwamnan a ofishin hukumar yaki da cin hanci da rashawa na Sakkwato tsawon awanni takwas a daidai lokacin rubuta wannan rahoton.

Wata majiya da aka nakalto a cikin rahoton ta ce:

“Ya amsa gayyatar a ofishin Sakkwato da misalin karfe 11 na safiyar Talata. An basa beli, amma bai iya cika sharuddan belin ba.”

KU KARANTA KUMA: Babbar magana: Tsohon minista Fani-Kayode ya sallami ma'aikacin sa saboda cin mutuncin Sambo Dasuki

A wani labarin, shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa, Abdulrasheed Bawa, ya roƙi yan Najeriya da su taimaka wajen yaƙi da cin hanci da rashawa saboda hukumarsa ba zata iya ita kaɗai ba.

Bawa ya faɗi hakane lokacin da ya karbi baƙuncin ƙungiyoyi masu zaman kansu a hedkwatar hukumar EFCC dake Abuja, ranar 19 ga watan Afrilu.

Ya ƙara da cewa Najeriya ƙasar mu ce dukkanmu, wadda muke alfahari da ita, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel