Babbar magana: Tsohon minista Fani-Kayode ya sallami ma'aikacin sa saboda cin mutuncin Sambo Dasuki
- An dakatar da wani mamba na kungiyar yada labaran Fani-Kayode
- Fani-Kayode ya ce ma’aikacin ya yi amfani da shafinsa na Twitter wajen tozarta tsohon NSA Dasuki
- Tsohon ministan ya bayyana Dasuki a matsayin amintaccen aboki ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan
Femi Fani-Kayode, tsohon ministan jirgin sama, ya dakatar da daya daga cikin mukarrabansa saboda amfani da shafinsa na Twitter wajen cin mutunci da kiran tsohon mai ba da shawara kan harkokin tsaro (NSA), Kanal Sambo Dasuki, maci amana da ya ci amanar tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan a 2015.
Legit.ng ta rahoto cewa Fani-Kayode, a cikin wani sakon Twitter a ranar Litinin, 19 ga Afrilu, ya ce wani mamba na kungiyar sa ya wallafa wani zargi a kafofin sada zumunta game da wadanda suka ci amanar Goodluck Jonathan a lokacin zaben 2015.
Ya ce Dasuki ya kasance mai biyayya ga Jonathan a duk tsawon shekaru hudu da ya yi yana NSA, ya kara da cewa an sauke ma'aikacin da ya yi kuskuren daga aikin sa.
Fani-Kayode yace:
“Col. Sambo Dasuki na daya daga cikin sunayen da aka ambata. Anyi wannan ba tare da izini na ba kuma cikin kuskure. Col. Dasuki amintaccen mamba ne na gwamnatin Jonathan. kuma tsawon shekaru 4 da yake tsare, na yi magana a kan sa fiye da kowa.
KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya gana da Sabon Sufetan yan sanda a karon farko bayan dawowarsa daga Landan
“Abin takaici ne kuma ba za a yarda da sunan nasa ba a cikin wannan jerin kuma na dakatar da wanda yayi wannan katobarar daga aiki.
“Baya ga gaskiyar cewa Col. Sambo Dasuki ya kasance babban aboki kuma dan’uwa, dangin Dasuki da Fani-Kayode suna da dadaddiyar dangantaka wacce ta gabaci wannan zamanin. Misali mahaifin Col. Dasuki, marigayi Sultan Ibrahim Dasuki, ya kasance na kusa sosai da nawa."
Tsohon ministan ya dage kan cewa Dasuki ba mayaudari bane, yana mai cewa tsohon NSA bai taba yin adawa da neman zaben Jonathan a 2015 ba.
Ya kara da cewa:
“Ya yi wa tsohon shugaban kasa Jonathan aiki a matsayin NSA cikin kwazo,da aminci. Ina nadamar duk wani abin kunya da wannan kuskuren ya haifar masa ko masoyinsa. An cire rubutun batancin."
KU KARANTA KUMA: Kar ku ragawa kowa: FG ta umurci ƴan sanda su hukunta masu tada zaune tsaye a Kudu
A wani labarin, a ranar Litinin, jami'ar Abuja (UniAbuja) tayi martani ga hukumar JAMB kan zargin da tayi cewa jami'ar na ɗaukar ɗalibai ba bisa ƙa'ida ba.
Hukumar JAMB ta zargi jami'ar ne saboda ƙin turama hukumar jerin sunayen waɗanda ta ɗauka kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.
A wani jawabi da UniAbuja ɗin ta fitar, ta bakin mai magana da yawunta, Dr Habib Yakoob, ya bayyana abinda kundin tsarin mulkin jami'o'i ya tanadar game da ɗaukar sabbin ɗalibai.
Asali: Legit.ng