EFCC ta kowa ce, Babu wanda ya isa ya juya ta, inji Abdulrasheed Bawa

EFCC ta kowa ce, Babu wanda ya isa ya juya ta, inji Abdulrasheed Bawa

- Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya yi kira ga yan Najeriya da su taimaka ma hukumarsa wajen gudanar da aikinta yadda ya kamata

- Bawa yace aikin yaƙi da cin hanci da kuma rashawa ba na hukumar EFCC kaɗai bane, aikine da kowa yakamata ya bada gudummuwarsa a ciki

- Shugaban Ya ce hukumarsa zata cigaba da aiki kafaɗa-da-kafaɗa da ƙungiyoyi masu zaman kansu, ɗai-ɗaikun mutane, da kuma masu ruwa da tsaki domin ganin ta yi nasara a ayyukanta

Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa, Abdulrasheed Bawa, ya roƙi yan Najeriya da su taimaka wajen yaƙi da cin hanci da rashawa saboda hukumarsa ba zata iya ita kaɗai ba.

KARANTA ANAN: PDP ta sake huro ma Pantami wuta, ta yi kira ga DSS ta gayyaci Ministan ya amsa tambayoyi

Bawa ya faɗi hakane lokacin da ya karbi baƙuncin ƙungiyoyi masu zaman kansu a hedkwatar hukumar EFCC dake Abuja, ranar 19 ga watan Afrilu.

A jawabin shugaban EFCC ɗin ya ce:

"EFCC ta kowa da kowa ce, ba ta wani mutum daya bace. Mun daɗe da gano cewa aikin EFCC ba zai yuwu ma hukumar ita kaɗai ba, Saida haɗin kan ƙungiyoyi masu zaman kansu, ɗai-ɗaikun mutane da masu ruwa da tsaki"

Ya ƙara da cewa Najeriya ƙasar mu ce dukkanmu, wadda muke alfahari da ita, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

EFCC ta kowa ce, Babu wanda ya isa ya juya ta, inji Abdulrasheed Bawa
EFCC ta kowa ce, Babu wanda ya isa ya juya ta, inji Abdulrasheed Bawa Hoto: @officialEFCC
Asali: Twitter

KARANTA ANAN: Yadda Mutum 20 suka mutu a hare-haren ramuwar gayya tsakanin Yan Bindiga da Jami'an Bijilanti

Bawa ya bada tabbacin EFCC zata haɗa kafaɗa-da-kafaɗa da ƙungiyoyi masu zaman kansu wajen ganin ta gudanar da ayyukanta yadda yakamata.

A ɓangarensa, mataimakin haɗakar ƙungiyoyin, Nse Victor Udeh, ya bayyana irin tasirin da cin hanci da rashawa ke dashi wajen hana ƙasa cigaba.

Ya ce: "Da ace ɓangaren lafiya a ƙasar nan na aiki yadda yakamata, ɓangaren Ilimi, tafiye-tafiye, hanyoyi da sauransu, to da Ba wani abu da zamu damu sosai akansa"

Ya ƙara da cewa cin hanci da rashawa ne ke daƙile duk wani yunƙuri na gyaran ƙasar nan ta kowanne ɓangare.

A wani labarin kuma Yan sanda sun kama wata mata da zargin ta kashe ɗan kishiyarta da guba

Rundunar yan sandan jihar Enugu ta kama wata matashiyar mata da zargin kisan ɗan kishiyarta.

Matar da ake zargin ta amsa laifinta, amma tace ta yi haka saboda mijinta baya bata kulawa sam da ita da yayanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: