Gwamnan Najeriya na shirye-shiryen barin kujerarsa, ya fice daga gidan gwamnati
- Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya mayar da martani game da kalubalen da Sanata Okorocha ya fuskanta kwanan nan
- Wike ya shawarci dan majalisar kan yadda zai magance matsalolin siyasarsa
- Kwanan nan ne hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta tsare Okorocha na tsawon awanni 48 kafin aka ba shi beli
Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bayyana cewa ya fice daga gidan gwamnati a shirye-shiryen barin ofis idan wa’adin mulkinsa ya kare a 2023.
Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, Wike ya bayyana hakan ne a wajen taron sunan wani yaro a Abuja, cewa ya san wasu tawagar siyasa za su biyo shi bayan ya bar mulki.
KU KARANTA KUMA: Manyan biloniya 5 masu saukin kai, suna wasa da ma’aikatansu da kuma yawan taimakon jama’a
Ya ce a shirye yake ya fuskanci irin wadannan matsalolin lokacin da ya sauka daga mukaminsa na gwamna.
Gwamnan ya bayyana cewa a halin yanzu Sanata Okorocha da danginsa suna cikin tsanantawa ta siyasa.
Ya shawarci sanatan da ya jajirce domin zai fita daga matsalolin da karfinsa, jaridar The Sun ta ruwaito.
Wike ya ce:
“Mahukuntan siyasa za su bibiye ka musamman bayan ka bar ofis saboda haka abin da kake fuskanta a yau ba sabon abu bane kan ka da iyalanka. Na san za su bibiyeni amma na shirya, na shirya masu.''
Sanata Rochas Okorocha ya yi magana game da yanayin da ya sa aka sake shi daga hannun hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati (EFCC).
KU KARANTA KUMA: Babbar magana: Tsohon minista Fani-Kayode ya sallami ma'aikacin sa saboda cin mutuncin Sambo Dasuki
A gefe guda, Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa, Abdulrasheed Bawa, ya roƙi yan Najeriya da su taimaka wajen yaƙi da cin hanci da rashawa saboda hukumarsa ba zata iya ita kaɗai ba.
Bawa ya faɗi hakane lokacin da ya karbi baƙuncin ƙungiyoyi masu zaman kansu a hedkwatar hukumar EFCC dake Abuja, ranar 19 ga watan Afrilu.
A jawabin shugaban EFCC ɗin ya ce: "EFCC ta kowa da kowa ce, ba ta wani mutum daya bace. Mun daɗe da gano cewa aikin EFCC ba zai yuwu ma hukumar ita kaɗai ba, Saida haɗin kan ƙungiyoyi masu zaman kansu, ɗai-ɗaikun mutane da masu ruwa da tsaki"
Asali: Legit.ng