Manyan biloniya 5 masu saukin kai, suna wasa da ma’aikatansu da kuma yawan taimakon jama’a

Manyan biloniya 5 masu saukin kai, suna wasa da ma’aikatansu da kuma yawan taimakon jama’a

Saukin kai abu ne da ba kasafai ake samunsa ba musamman a cikin manyan masu kuɗi amma akwai masu kuɗi da lokuta da dama suka nuna cewa arziki da tawali'u na iya tafiya tare.

Legit.ng ta zakulo wasu manyan masu kudi wadanda suka banbanta kansu ta hanyar yin mu'amala da ma'aikatansu, saukin kansu da kuma ayyukan jin kai da suke yiwa al'umma.

KU KARANTA KUMA: Mako biyu da yin aurenta amarya ta fara korafi, ta ce mijinta yana aikenta barkatai

Manyan biloniya 5 masu saukin kai, suna wasa da ma’aikatansu da kuma yawan taimakon jama’a
Manyan biloniya 5 masu saukin kai, suna wasa da ma’aikatansu da kuma yawan taimakon jama’a Hoto: anuarbekiman, OvieNews
Asali: Twitter

1. Jeff Bezos

Yana da kyau mu fara da mai kudin duniya duk da cewa jerin ba wai na matsayin kuɗi bane.

A cewar Market Insider, an gano Jeff Bezos kwananki a cikin wasikar sa ta shekarar da ta gabata yana ba da shawarar rayuwa ga ma'aikatan sa.

A cikin wannan yanayi ya kuma sha alwashin taimakawa ma'aikatansa. Babu shakka wannan ya inganta ƙudurinsu sannan kuma ya karfafa masu gwiwa.

2. Bill Gates

Wanda ya kirkiri Microsoft, attajiri kuma mai taimakon jama'a Bill Gates a cikin shekarar 2018 ya baiwa wa wasu daliban kwalejin Amurka da aka yaye daya daga cikin mahimman litattafan da ya taba karantawa, a cewar GeekWire.

Gates ya bayyana littafin mai suna Factfulness daga Hans Rosling a matsayin "jagora mai kyau game da tunanin duniya."

Kasancewar ya fito daga hannun hamshakin mai kuɗi, daliban ba za su yi saurin mantawa da irin waɗannan kyaututtukan ba.

KU KARANTA KUMA: Rikita rikita: Wasa ya ƙwace yayin da Gwamnan Kano Ganduje ya hau babur ɗin KAROTA da babbar riga

3. Elon Musk

An gano shugaban Tesla kuma mutum na biyu a masu arzikin duniya Elon Musk a cikin wata mota mara kyau da gyaran gashi mara fasali yayin da ya ziyarci ma’aikatansa a ma’aikatar sa ta Texas. Musk ya kai ziyarar ne don yin ma'amala da ma'aikatan da ke kera motocin lantarki.

Masoyan Musk da ma'aikata sun nadi lokacin sannan suka watsa shi a shafukan soshiyal midiya. Shin mai zai karfafa maka gwiwar yin aiki sama da wannan?

4. Aliko Dangote

An gano shahararren attajirin nan kuma mai kudin Afirka Aliko Dangote kwanan a cikin bidiyo yayin da yake ganawa da ma’aikatan sa. Abin da ya sa bidiyon ya yadu shi ne yadda ya ke karfafa masu gwiwa yayin da yake magana.

5. Femi Otedola

Wani hamshakin attajirin dan Najeriya kuma mai taimakon jama'a Femi Otedola ya fidda naira biliyan 5 yayin da ya tallafawa gidauniyar taimako na 'yarsa.

Dan kasuwar man fetur din ya ba da gudummawar ne a wurin bikin gidauniyar da ya halarta. Abin sha'awa shine, Aliko Dangote ma ya tallafawa gidauniyar a wannan lokacin da Naira miliyan 100.

A wani labari na daban, ministan sadarwa da tattalin arziƙin zamani, Dr. Isa Pantami yace amfani da ayyukan fasahohin Zamani (IT) ya samar ma Nageriya rarar kuɗi kimanin 22.5 biliyan.

Ministan ya faɗi hakane a bikin cika shekara 20 da kafa hukumar samar da cigaba ta hanyar fasahar zamani (NITDA) wanda akai ma take da NITDA@20 ranar Litinin a Abuja, Dailytrust ta ruwaito.

Pantami yace duk da an ƙirƙiri NITDA a watan Afrilun shekarar 2001 a matsayin wani sashi na ma'aikatar sadarwa, ta cigaba da haɓaka har tazama tafi kowacce hukuma gudanar da ayyuka ga gwamnatin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel