Karatu, gidan soja, da juyin mulki; Abubuwa 8 da ya kamata kowa ya sani game da Idris Deby

Karatu, gidan soja, da juyin mulki; Abubuwa 8 da ya kamata kowa ya sani game da Idris Deby

A makon nan ne ake jimamin mutuwar Idriss Déby Itno. Kafin rasuwarsa, ya kasance shugaban Chad, wanda ya shafe sama da shekara 30 a mulki.

Legit.ng Hausa ta tsakuro wasu bayanai a kan tarihin rayuwar Idriss Déby Itno daga shafin Britanica.

1. Haihuwa

An haifi Idriss Déby Itno a shekarar 1952 a wani gari da ake kira Fada a kasar Chadi. Marigayi Idriss Déby Itno ya mutu ya na mai shekara 68.

Deby ya na cikin mutanen kabilar the Zaghawa da su ke yankin Ennedi a Arewacin kasar Chadi.

2. Karatu

A farkon shekarun 1970 ne Idriss Déby ya shiga gidan soja, a wancan lokaci kasarsa ta na cikin yakin basasa. A 1976 ya tafi kasar Faransa ya yi karatun iya tuka jirgin sama.

Kara karanta wannan

Kwankwaso @66: Wasu abubuwa 10 da ba ka sani ba a game da ‘Dan Takaran NNPP

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

3. Shiga siyasa

Bayan dawowarsa gida a 1978, ya mara wa shugaban dakarun ‘yan taware, Hissène Habré baya. A karshe Habré ya yi nasarar karbe mulki a 1982, ya zama shugaban Chadi.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe Shugaban kasar Chadi

4. Suna

Marigayin ya samu shahara a sakamakon juyin mulkin Hissène Habré, daga nan aka nada shi a matsayin shugaban hafsun soja, ya kuma tafi kasar Faransa ya kara karatu.

5. Juyin-mulki

A farkon 1989 aka soma zargin Déby da shirin kifar da gwamnatin Habré, wannan ya sa ya tsere zuwa Sudan. Daga Darfur, Déby ya shirya rundunar da ta kifar da gwamnati.

6. Shugaban kasan Soji

Bayan ya yi nasarar hambarar da Hissène Habré a 1990, Idris Déby ya dare kan mulki, ya dakatar da tsarin mulki. Déby ya yi alkawarin gyara kasar da kuma dawo da siyasa.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Gwamnati Ta Tanadi N470bn Don Karawa Malaman Jami'a Albashi Da Gyara Jami'a

7. …Ya rikida

A wani taron kasa da aka yi a 1993 sai Déby ya zama shugaban kasa na rikon kwarya. A shekarar 1996 aka tsara sabon kundin tsarin mulki, kuma ya shiga zabe, ya yi nasara.

Karatu, Soja, da juyin mulki; Abubuwa 8 da ya kamata ka sani game da Idris Deby
Idris Deby a lokacin yakin zabe
Asali: Twitter

KU KARANTA: COVID-19 da karyewar mai ya jawo tattalin arzikin Najeriya ya sukurkuce

8. Tazarce

Duk da koke-koken jama’a, Déby ya cigaba da zama a kan mulki, ya na lashe duka zabukan da aka gudanar a 2011, 2006, 2011 har zuwa zaben da aka yi a shekarar nan.

Dazu kun ji cewa bayan bada sanarwar mutuwar Idris Deby a filin daga, Sojin kasar Chadi sun nada 'dan marigayin, Mahamat Kaka, ya zama shugaban rikon kwarya.

Janar Mahamat Idriss Deby Itno mai shekaru 37 da haihuwa ne ya dare kujerar mahaifinsa, Idris Deby, a matsayin mukaddashin shugaban kasa kafin a shirya zabe.

A baya, gwamnati ta yi wa dokar kasar kwaskwarima ta yadda Deby zai iya cigaba da mulki har 2033.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng