Yanzu Yanzu: Buhari ya yi sabon nadi mai muhimmanci a bangaren shari’a

Yanzu Yanzu: Buhari ya yi sabon nadi mai muhimmanci a bangaren shari’a

- Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi majalisa ta amince da nadin Jastis Salisu Garba a matsayin babban alkalin babbar kotun birnin tarayya

- Hakan na kunshe ne a cikin wasikar da Buhari ya aike wa majalisar wanda Lawan Ahmed ya karanto a zauren yayin zamansu na yau Talata

- Jastis Garba ya fito ne daga karamar hukumar Malumfashi da ke jihar Katsina

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar dattawa da ta duba tare da amincewa da Mai Shari'a Salisu Garba don nada shi mukami a matsayin babban alkalin babbar kotun birnin tarayya.

Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya karanta wasikar Buharin a yayin zaman majalisar, jaridar The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Rikita rikita: Wasa ya ƙwace yayin da Gwamnan Kano Ganduje ya hau babur ɗin KAROTA da babbar riga

Yanzu Yanzu: Buhari ya yi sabon nadi mai muhimmanci a bangaren shari’a
Yanzu Yanzu: Buhari ya yi sabon nadi mai muhimmanci a bangaren shari’a Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

Shugaban Alkalan Najeriya (CJN), Mai Shari'a Tanko Muhammad, a watan Janairun 2021, ya rantsar da Mai Shari'a Garba a matsayin mukaddashin babban alkalin babbar kotun birnin tarayya.

Wannan ya biyo bayan ritayar mai shari'a Ishaq Bello daga matsayin babban alkali na Babban Kotun FCT.

Garba ya fito ne daga karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina.

Ya zama cikakken lauya a 1984 kuma ya kammala bautar kasa (NYSC) a 1985.

An nada Garba a matsayin Alkalin Majistare a birnin tarayya a 1989.

KU KARANTA KUMA: Kar ku ragawa kowa: FG ta umurci ƴan sanda su hukunta masu tada zaune tsaye a Kudu

Ya zama babban magatakarda na babban kotun tarayyar a 1997. An nada shi Alkalin Babban Kotun tarayya a 1998.

A wani labarin, Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya gana da sabon Sufetan yan sanda na riko, Usman Alkali Baba, a karon farko tun bayan dawowarsa daga Landan.

Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da shafin gwamnatin tarayya ya fitar a dandalin sada zumunta na Tuwita yau Litinin.

An dai naɗa, Usman Alkali Baba, a matsayin sabon sufetan Yan sanda yayin da shugaban ƙasa yake a Landan, inda yaje domin duba lafiyarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel