Shugaba Buhari ya gana da Sabon Sufetan yan sanda a karon farko bayan dawowarsa daga Landan

Shugaba Buhari ya gana da Sabon Sufetan yan sanda a karon farko bayan dawowarsa daga Landan

- Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya gana da sabon Sufetan yan sanda na riko, Usman Alkali Baba, a karon farko tun bayan dawowarsa daga Landan.

- Wannan na kunshe ne a wata sanarwa da shafin gwamnatin tarayya ya fitar a dandalin sada zumunta na Tuwita yau Litinin

- An dai naɗa, Usman Alkali Baba, a matsayin sabon sufetan Yan sanda yayin da shugaban ƙasa yake a Landan, inda yaje domin duba lafiyarsa

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya gana da sabon sufetan yan sandan ƙasar nan na riƙo, Usman Alƙali Baba, a karon farko tun bayan dawowarsa daga Landan.

KARANTA ANAN: PDP ta sake huro ma Pantami wuta, ta yi kira ga DSS ta gayyaci Ministan ya amsa tambayoyi

Shugaban ya gana da sufetan ne a fadar sa dake babban birnin tarayya Abuja da yammacin ranar Litinin.

Wannan na kunshe ne a wani saƙo da shafin gwamnatin tarayya na dandalin sada zumunta Tuwita ya fitar.

An dai naɗa sabon sufetan ne yayin da shugaban ƙasa Buhari ke ƙasar Burtaniya inda yaje domin duba lafiyarsa.

Ministan harkokin rundunar yan sanda, Maigari Dingyadi, shine ya bayyana naɗin, Usman Alkali Baba, a matsayin sufetan yan sanda na riƙo.

Da Ɗuminsa: Shugaba Buhari ya gana da Sabon Sufetan yan sanda a karon farko bayan dawowarsa daga Landan
Da Ɗuminsa: Shugaba Buhari ya gana da Sabon Sufetan yan sanda a karon farko bayan dawowarsa daga Landan Hoto: @NigeriaGov
Asali: UGC

KARANTA ANAN: Zaɓen 2023 bazai yuwu ba matuƙar ba'a magance matsalar tsaro ba, Inji tsohon Daraktan DSS

Naɗin sabon sufetan ya baiwa yan Najeriya mamaki, bayan shugaba Buhari ya ƙara ma tsohon sufetan, Muhammad Adamu, watanni uku, kafin wa'adin ya ƙare kuma aka sabule shi daga kan muƙaminsa.

Sai-dai ana zargin cewa an cire tsohon sufetan ne saboda jerin hare-hare da aka kai gidan gyaran hali da kuma hedkwatar yan sanda a yankin kudancin ƙasar nan.

Minista Maigari Dingyaɗi ya bayyana cewa an dakatar da wa'adin tsohon sufetan ne bayan gama bin matakan zaɓo sabon sufetan. Amma duk da haka ana zargin harin da yan bindiga suka kai gidan gyaran hali ne yayi sanadiyyar sauke shi.

A wani labarin kuma Gwamnatin tarayya zata ɗauki sabbin sojoji domin ƙarfafa yaƙi da Boko Haram, Ministan Tsaro

Ministan tsaro yace gwamnatin tarayya na shirye-shiryen ɗaukar sabbin sojoji waɗanda zasu taimaka wajen yaƙi da ta'addanci

Bashir Magashi ya bayyana haka ne yayin da ya jagoranci tawagar shugabannin tsaro suka kai ziyara ga rundunar sojojin 'Operation Lafiya Dole'.

Asali: Legit.ng

Online view pixel