Wani jigon jam'iyyar APC ya bukaci Buhari ya gaggauta tsige Dr Pantami

Wani jigon jam'iyyar APC ya bukaci Buhari ya gaggauta tsige Dr Pantami

- Zargin da ya dabaibaye ministan yada sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr. Isa Pantami har yanzu yana kan aiki

- Wani jigo a jam’iyyar APC, Cletus Obun, ya ce ya kamata ministan ya yi murabus ko kuma a tsige shi

- Jigon na jam'iyyar APC ya kamanta lamarin Dr Pantami da abinda ya faru da tsohuwar ministan kudi Adeosun

Wani jigo a jam’iyyar APC, Cletus Obun, ya yi kira da a kori ko a tursasa murabus ga ministan yada sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr. Isa Pantami.

Obun ya yi wannan kiran ne a ranar Litinin, 19 ga Afrilu yayin da yake magana a wani shirin kumallo na gidan Talabijin mai zaman kansa na Afirka.

Ya bayyana cewa ya kamata a kori Dr Pantami daga mukamin sa idan har ba ya son yin murabus duba da abubuwan da aka bayyana game da shi.

KU KARANTA: Lai Mohammed ya caccaki masu son a raba kasa, ya ce rikici na bullowa zasu tsere

Wani jigon jam'iyyar APC ya bukaci Buhari ya gaggauta tsige Dr Pantami
Wani jigon jam'iyyar APC ya bukaci Buhari ya gaggauta tsige Dr Pantami Hoto: 1.bp.blogspot.com
Asali: UGC

Ya kamanta batun da murabus din tsohuwar ministar kudi Kemi Adeosun, wacce ta bar ofishinta kan jabun takaddun bautar kasa.

A kalamansa ya ce: “Duba batun Pantami misali. Me Adeosun ta yi? Ba ta jira an kore ta ba. Murabus Ta yi.

“Pantami ya kamata ya yi murabus, idan bai yi hakan ba, ka kore shi! Ba wai ba da alama cewa ka jure kuma kana jure ba wa gwamnati suna mara kyau ba. Me yasa har yanzu Pantami zai zauna a ofis.”

KU KARANTA: Duk da kasancewarsa a kurkuku, Zakzaky ya yi rabon abincin Ramadana ga mabukata

A wani labarin, Kwamitin hadin gwiwa kan kungiyoyin fararen hula da lamuran addini na Najeriya, ya yi Allah wadai da zargin alaka da kungiyoyin 'yan ta'adda da aka yi wa ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr Isa Ali Ibrahim Pantami.

Shugaban kwamitin, Bishop John Okafor, ya bayyana matsayarsu a cikin wata sanarwa da jaridar Vanguard ta ruwaito kuma Legit.ng ta gani a ranar Litinin, 19 ga Afrilu.

Wani bangaren, sanarwar na cewa: “Kwamitin bayan bincike ya gano cewa zarge-zargen da ake yi a kansa an yi su ne da nufin bata shi a matsayinsa na minista da kuma taba mutuncin kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel