Yanzu-Yanzu: Buhari ya karbi bakuncin sabon shugaban Nijar a Abuja

Yanzu-Yanzu: Buhari ya karbi bakuncin sabon shugaban Nijar a Abuja

- Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin shugaba Mohamed Bazoum a Abuja

- Shugabannin biyu sun shiga taron sirri jim kadan bayan isowar Bazoum

- Bazoun wanda aka rantsar a Afrilun ya zo Nigeria ne ziyarar aiki na kwanaki biyu

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya karbi bakuncin takwararsa na Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum a fadar gwamnati da ke Abuja.

Buhari ya tarbi bakonsa, wanda ya zo Nigeria ziyarar aiki na kwanaki biyu a fadar Aso Rock misalin karfe 1.22 na rana.

Yanzu-Yanzu: Buhari ya karbi bakuncin sabon shugaban Nijar a Abuja
Yanzu-Yanzu: Buhari ya karbi bakuncin sabon shugaban Nijar a Abuja. Hoto: @BayoOmoboriowo
Asali: Twitter

Cikin wadanda suka taya shugaban kasar tarbar Bazoum akwai shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, FCT, Mohammed Bello da wasu hadiman shugaban kasa.

DUBA WANNAN: An yi tonon asiri tsakanin sojoji da wasu fararen hula kan taimakon ƴan Boko Haram

Gwamnonin jihohin Sokoto, Borno, Kebbi, Yobe da Zamfara suma suna fadar ta shugaban kasa domin maraba da Bazoum wanda aka rantsar da shi a mulkinsa karo na farko a matsayin shugaban Nijar a ranar 2 ga watan Afrilun 2021.

Rantsar da Bazoum ne karo na farko da aka mika mulki daga shugaban mai barin garo na Nijar tun bayan da kasar ta samu yanci a shekarar 1960.

KU KARANTA: Hotunan wasu ƴan Nigeria da suka sake karɓar addinin musulunci a Libya

Shugabannin kasashen Yammacin Afrikan biyu sun shiga taron sirri jim kadan bayan bukukuwar maraba da shi.

Buhari da Bazoum sun sha ruwa tare a fadar shugaban kasa misalin karfe 6.50 na yamma.

Kafin zuwan shugaban na Nijar, Buhari ya gana da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo.

A ranar Alhamis ne Buhari ya dawo daga Birtaniya inda ya tafi hutu na kwanaki 16.

A wani labarin daban, direbobin motoccin haya da ke bin titin Gusau zuwa Dansadau a jihar Zamfara sun shiga yajin aikin sai baba ta gani saboda yawaitar fashi da makami da garkuwa da ke yawan faruwa a hanyar, Daily Trust ta ruwaito.

Titin ya kasance wayam babu motocci tun kwanaki hudu da suka gabata domin direbobin sun ki fitowa aiki.

Shugaban kungiyar direbobi na kasa reshen Dansadau, Isihu Ticha ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa sun shiga yajin aikin ne domin janyo hankalin mahukunta kan halin da suke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164