An cafke wasu mutum biyu da ke yi wa ƴan bindiga aikin 'likitanci' a Kaduna

An cafke wasu mutum biyu da ke yi wa ƴan bindiga aikin 'likitanci' a Kaduna

- Jami'an tsaro sun kama wasu mutum biyu da ke yi wa yan bindiga magani

- Mr Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna ya sanar da hakan

- Ya kuma ce yan bindiga sun halaka mutane biyu a wurare biyu a jihar na Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce yan sanda sun kama mutane biyu da ake zargin suna yi wa yan bindiga magunguna a Buruku a karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna.

Gwamnatin ta ce a kalla mutane uku ne yan bindiga suka kashe a wurare daban daban a jihar cikin awanni 48, Vanguard ta ruwaito.

An kama wasu mutane biyu da ke yi wa 'yan bindiga magani
An kama wasu mutane biyu da ke yi wa 'yan bindiga magani. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: An yi tonon asiri tsakanin sojoji da wasu fararen hula kan taimakon ƴan Boko Haram

Kwamishinan tsaro a harkokin cikin gida na jihar, Mr Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar a Kaduna.

A cewarsa, a daya daga cikin harin, yan bindigan sun kai hari kauyen Rafin Roro a karamar hukumar Kajuru inda suka kashe mutum daya.

Ya ce an gano harsashi 11 na AK-47 kuma jami'an tsaro na cigaba da bincike.

KU KARANTA: Okorocha ya ce wani sarki daga Arewa da gwamna a Kudu suka fito da shi daga hannun EFCC

"Kazalika, yan bindigan sun kashe wani mutum daya a wani gari kusa da Maraban Jos a karamar hukumar Igabi.

"Yan bindigan sun kuma kashe wani mutum daya a wajen kauyen Garu, karamar hukumar Igabi, bayan sace shanu mallakar wasu mutane biyu."

Kwamishinan ya ce jami'an tsaro sun fafata da yan bindigan, kuma sun gano daya yana yawo a daji yayin da saura suka tsere da raunin harsashi.

Ya ce gwamnan jihar Nasir El-Rufai ya nuna bacin ransa a yayin da ya yi addu'a Allah ya jikan wadanda suka rasu, ya kuma yi wa iyalansu ta'aziyya.

"Gwamnan ya jinjinawa yan sandan na jihar Kaduna bisa kamen a karamar hukumar Chikun ya kuma bukaci su cigaba da bincike kan lamarin."

A wani labarin daban, direbobin motoccin haya da ke bin titin Gusau zuwa Dansadau a jihar Zamfara sun shiga yajin aikin sai baba ta gani saboda yawaitar fashi da makami da garkuwa da ke yawan faruwa a hanyar, Daily Trust ta ruwaito.

Titin ya kasance wayam babu motocci tun kwanaki hudu da suka gabata domin direbobin sun ki fitowa aiki.

Shugaban kungiyar direbobi na kasa reshen Dansadau, Isihu Ticha ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa sun shiga yajin aikin ne domin janyo hankalin mahukunta kan halin da suke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164