Azumin watan Ramadana ne ya sa 'yan bindiga suka rage kai hari, Tsohon Daraktan DSS
- Wani tsohon darakta a hukumar DSS ya bayyana cewa, 'yan bindiga sun yi likimo ne saboda Azumi
- Ya ce Azumin watan Ramadana ne ya sa suka rage kai hare-hare kan al'ummar fadin kasar
- Ya ce su ma kansu 'yan bindigan suna addu'o'i a watan Ramadana don haka suka rage kai hari
Wani tsohon Daraktan DSS, Mista Mike Ejiofor a ranar Litinin ya ce ragin hare-hare da aka samu na ’yan bindiga a duk fadin kasar na iya kasancewa sanadiyyar azumin Ramadana da ake gudanarwa a yanzu a fadin kasar.
Ramadana shi ne wata na tara a kalandar Musulunci, wanda Musulmai a duk duniya suke azumta, yin addu’o'i, komawa ga Allah, da kuma nuna soyayya ga jama’a, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.
Sarkin Musulmi a makon da ya gabata ya yi ishara ga fara azumin Ramadana, bayan ganin wata.
KU KARANTA: Nasara daga Allah: 'Yan sanda sun sheke 'yan bindiga 6 a jihar Neja
Mista Ejiofor ya ce: "('Yan ta'addan) ba wai sun sauko bane."
“Akwai lauje cikin nadi, musamman a Arewa maso Yamma; kun san muna azumi yanzu. Don haka wannan ke da alhakin abin da muke tsammanin ke sassauta batutuwan 'yan bindiga, musamman a yankin Arewa maso Yamma inda ya fi yawa.
“Wasu daga cikinsu ma suna Sallah. Mutane ne masu addini. Ba zuwa su kai daga sama ba. A wasu lokuta, su ma suna so su yi addu'a ga Allah. Hatta dan fashi da makami zai yi addu’ar Allah ya kubutar da shi daga ayyukansa.”
Najeriya na fama da jerin matsalolin tsaro wadanda suka hada da ta'addanci, 'yan bindiga, kungiyoyin asiri da sauransu a wasu sassan kasar.
Kasar ta dade tana yaki da ta'addanci fiye da shekaru goma wanda ya yi sanadiyyar kashe mutane sama da 36,000 tare da raba dubunnan daruruwa da muhallansu a arewa maso gabas.
KU KARANTA: Rikicin kabilanci ya sake ballewa a wani yankin jihar Gombe, an kona gidaje 50
A wani labarin daban, Yayin da Najeriya ke yaki da ‘yan ta’addan Boko Haram a yankin arewa maso gabas, Ministan Tsaro, Magashi Bashir, ya nemi rundunar Operation Lafiya Dole da kada su ji tsoron harbe-harbe daga 'yan ta’addan, gidan talabijin na Channels ya ruwaito.
Ya ba da wannan umarnin ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin wata ziyara da ya kai wa rundunar a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, tare da shugaban hafsan hafsoshin tsaro, Janar Lucky Irabor da sauran shugabannin rundunonin tsaro.
"Kada ku ji tsoron kowane harsashi, harsashin zai zo kuma zai tafi," in ji shi.
Asali: Legit.ng