'Yan matan Chibok da aka sake da yawansu suna can suna karatu a jami'a, Tallen

'Yan matan Chibok da aka sake da yawansu suna can suna karatu a jami'a, Tallen

- Ministar Mata ta bayyana cewa, 'yan matan Chibok na can Jami'a suna ci gaba da karatunsu

- A cewarta, da yawansu sun shiga jami'a wasu kuwa suna kokarin rubuta jarrabawar WAEC

- Ta kuma shaida irin kwazo da 'yan matan ke dashi da kuma aiki tukuru a makaratun da suke

Ministar Harkokin Mata, Pauline Tallen, ta ce ‘yan matan makarantar Chibok da aka sako suna da kwazo a makarantu kasancewar wasu sun riga sun shiga jami’a wasu kuma sun shirya rubuta jarabawar kammala sakandare (SSCE), The Nation ta ruwaito.

Tallen ta bayyana hakan ne a Abuja a ranar Alhamis a yayin sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) tare da kungiyar kula da ‘yan gudun hijira ta duniya (IOM), inda ta ce ita da kanta ta ziyarci 'yan matan a makaranta.

“Ina farin cikin sanar da ku duka cewa wadanda aka saka suna aiki tukuru a makaranta. Na dai je na ziyarce su a Jami’ar Amurka ta Najeriya dake Yola.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: Najeriya ce ta 1 a shigo da kayayyaki daga kasashen waje, WTO

'Yan matan Chibok da aka sake da yawansu suna can suna karatu a jami'a, Tallen
'Yan matan Chibok da aka sake da yawansu suna can suna karatu a jami'a, Tallen Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

“Na ziyarce su kuma na yi kwana daya tare da su makonni hudu da suka gabata, muna da kusanci da shugabannin makarantar.

“Suna da kwazo a makaranta, wasu daga cikinsu sun sami shiga jami’a, wasu kuma suna shirin rubuta WAEC."

Tallen ta ce tare da goyon baya daga Shugaba Muhammadu Buhari, ta jagoranci wata tawaga mai karfin gaske zuwa Chibok a shekarar 2020 inda ta gana da iyayen ‘yan matan da har yanzu ke hannun 'yan ta'addan.

Ta ce a yayin ziyarar, ta isar da tabbacin Gwamnatin Tarayya cewa ba a manta da ‘yan matan da har yanzu ba a sako su ba.

“Muna aiki tare da wakilan al’ummar Chibok don bai wa matasa mata da danginsu sabuwar rayuwa.

"Muna kuma aiki tare da Ma'aikatar Kula da Jin Kai da ci gaban zamantakewar jama'a ta tarayya don tabbatar da cewa 'yan matan da danginsu sun sami cikakken gyara kuma an dawo da martabarsu," in ji ta.

KU KARANTA: Rashin kwarewar Buhari a mulki ne ya sa Twitter ta kai hedkwatarta Ghana, PDP

A wani labarin, Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya ce akwai alamu masu karfi da ke nuna cewa wasu jami’an gwamnatin Najeriya na hada baki da masu satar mutane don aikata mummunan aikinsu, Arise Tv ta ruwaito.

Mista Ortom ya ce 'yan siyasar da ke da wata manufa sun shigo da sojojin haya na kasashen waje don taimaka musu su ci zaben 2019. Ya lura cewa watsi da wadannan sojojin haya shi ya haifar da tabarbarewar yanayin tsaro a kasar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis lokacin da yake gabatar da lacca a Makon 'Yan Jaridu na 2021 mai taken: "Rashin tsaro a Najeriya: Maido da Zaman Lafiya, Hadin kai da Ci gaba" kuma kungiyar Hadin kan 'Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) ta shirya.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel