Da dumi-dumi: Najeriya ce ta 1 a shigo da kayayyaki daga kasashen waje, WTO
- Rahoton kungiyar kasuwanci ta duniya ya ce Najeriya ce ta 1 fannin shigo da kayayyaki daga kasashen waje
- Rahoton ya fito ne a yau Juma'a, in da ya lissafo wasu kasashen ciki har da Burtaniya da Amurka
- A rahoton an kawo kasashen da ke fitar da kayayyaki, ciki har da kasa daya a Afrika amma ban da Najeriya
Najeriya ita ce kasa ta farko da ke shigo da kayayyakin kasuwanci a Afirka a shekarar 2020, bayanan da Kungiyar Kasuwanci ta Duniya ta fitar a ranar Juma'a, The Punch ta ruwaito.
Kungiyar cinikayyar kasa da kasa da ke da hedikwata a Geneva ta sanya Najeriya a matsayi na 25 da ke shigo da kayayyakin kasuwanci a duniya kuma kasa ta daya a shigo da kasuwanci a Afirka sai Masar wacce ta kasance ta 28 a duniya.
KU KARANTA: Akwai hannun manyan 'yan siyasa a yawan sace-sacen mutane, gwamna Ortom
Yayin da Masar da Morocco suka shiga sahun masu fitar da kaya a duniya karkashin jagorancin Amurka, Najeriya ta kasance ba a bayyana ta a cikin jerin masu fitar da kayayyakin kasuwanci a duniya ba.
Hakanan Amurka ta kasance ta farko a cikin jerin masu shigo da kayayyakin kasuwanci sannan China, Burtaniya da Japan suka biyo baya; yayin da Amurka, Burtaniya, China da India suka kasance a kan gaba a jerin masu fitar da kaya.
WTO ta lura cewa kiyasin farko ya dogara ne da alkaluman kwata-kwata.
Sakateriyar ta kiyasta wasu adadi na kasashe da yankuna da dama.
“Ba a samu bayanan shekarar 2020 ba ga Hadaddiyar Daular Larabawa. A shekarar 2019, an fitar da kayayyakin kasuwanci zuwa dala biliyan 72 kuma ana shigo da shi da dalar Amurka biliyan 73.”
KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Hukumar NAFDAC ta tsunduma yajin aikin gargadi ga gwamnati
Rahoton ya bayyana tashin farashin daga 17.33% zuwa 18.17% a tsakanin watannin Fabrairu da Maris na wannan shekarar ta 2021.
Domin amsa tambayoyin da 'yan Najeriya kan iya yi game da dalilan da ke jawo hauhawar farashin kayayyaki, wakilinmu a Legit.ng Hausa ya tattauna da wani masanin tattalin arziki daga kamfanin One 17 Capital Limited, Ismail Rufai.
Asali: Legit.ng