Yanzu yanzu: Sojojin Najeriya sun farma mabuyar 'Yan fashi a Benuwe, sun kashe 5

Yanzu yanzu: Sojojin Najeriya sun farma mabuyar 'Yan fashi a Benuwe, sun kashe 5

- Wasu da ake zargin ‘yan fashi ne sun kai hari garin Anune a karamar hukumar Makurdi ta jihar Benuwe

- Sai dai kuma, sojojin Najeriya sun kai farmaki maboyar 'yan ta'addan inda suka kashe biyar daga cikinsu

- Wasu jami'an 'yan sandan Najeriya sun bukaci al'ummar Binuwai da su guji karya doka da oda

Sojojin Operation Whirl Stroke (OPWS) sun kashe wasu yan fashi da makami su biyar da suka kai hari kan wani gari a ƙaramar hukumar Makurdi ta jihar Benuwe, Daily Trust ta ruwaito.

Jaridar ta ce sojojin sun kai farmaki maboyar ‘yan fashin a kan iyakokin jihohin Benuwe da Nasarawa a ranar Asabar, 17 ga Afrilu.

KU KARANTA KUMA: Ni ba dan ta'adda bane; direba na da sakatariya ta Kiristoci ne, Pantami

Yanzu yanzu: Sojojin Najeriya sun farma mabuyar 'Yan fashi a Benuwe, sun kashe 5
Yanzu yanzu: Sojojin Najeriya sun farma mabuyar 'Yan fashi a Benuwe, sun kashe 5 Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa yan fashin sun far ma mazauna kauyen Anune, wani garin karkara a wajen karamar hukumar Makurdi, kuma sun kashe wasu mutane da ba a bayyana adadin su ba.

Wani ganau ya ce an ga wani jirgin sojin sama mai saukar ungulu yana shawagi a kusa da kauyen da abin ya shafa tsakanin karfe 9 na safe zuwa 10 na safiyar Asabar, a daidai lokacin da sojoji da ‘yan sanda ke ta yawo a cikin manyan motoci.

Shaidar ya kara da cewa jami'an tsaro sun shiga cikin dajin da 'yan ta'addan suka tsere sannan kuma ba da dadewa ba, sai aka ga sojoji ’sun dawo tare da akalla gawarwakin mutane biyar da ake zargin na yan fashin ne.

A halin da ake ciki, kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar Benuwe, DSP Catherine Anene, ta tabbatar da harin kan kauyen Anune amma ba ta bayyana ko akwai wadanda suka rasa rayukansu ba.

KU KARANTA KUMA: Na sauya masu tsattsauran ra'ayi sama da 1000 tare da koyarwar addinin Islama, Pantami ya fadawa 'yan Najeriya

Anene ta ce an tura tawagar jami'an 'yan sanda yankin don dakile ci gaba da karya doka da oda.

A wani labarin, rundunar yan sanda reshen jihar Enugu ta kama wata mata yar shekara 29, Nnenna Egwuagu, da zargin kashe ɗan kishiyarta dan shekara uku, Wisdom Egwuagu.

Lamarin ya faru ne a garin Umulumgbe dake ƙaramar hukumar Idi, jihar Enugu ranar 9 ga watan Afrilu kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa matar da ake zargin ta baiwa yaron wani abu dake ɗauke da guba, kuma hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng