Na sauya masu tsattsauran ra'ayi sama da 1000 tare da koyarwar addinin Islama, Pantami ya fadawa 'yan Najeriya
- Rayuwar mutane da yawa da suka zama batattu sun ga haske bayan koyarwar Pantami
- A cewarsa, sama da mutum 1000 masu tsattsauran ra'ayi sun tuba ta sanadiyarsa
- Ku tuna cewa wasu kafofin yada labarai sun ruwaito cewa yana cikin jerin mutanen da Amurka ke zargi da ta’addanci
Da alama Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani, Isa Pantami, ya yi wa Najeriya alheri matuka da koyarwar addinin Islama.
A cewar Ministan, ta hanyar koyarwarsa, kimanin masu tsattsauran ra'ayi 1000 sun ga haske kuma sun tuba daga tsattsauran ra'ayinsu.
KU KARANTA KUMA: Ku tsammaci ci gaba, Buhari ya fadawa yan Najeriya a lokacin da ya dawo daga Landan
Ministan ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da yayi da jaridar Premium Times biyo bayan rahotannin da ke cewa yana cikin jerin mutanen da Amurka ke zargi da ta’addanci.
Harma, Pantami ya ce mutane da yawa waɗanda suka bar jami'a sun dawo don kammala karatunsu biyo bayan koyarwarsa.
Ya ce: "Amma wadanda suka rayu tare da ni a yankin Arewa maso gabashin kasar nan za su gaya muku duk tattaunawata nayi su ne tare da mutane, har ma da yin musu da su. A lokacin mutane suna jin tsoro, mun yi nasarar zama ido da ido sannan muka ce toh, bari mu zo mu yi muhawara'.
"Mun yi jayayya kuma mun yi muhawara, kuma an nadi waɗannan muhawara. Kuma saboda wannan, mutane da yawa sun watsar da akidunsu na tsattsauran ra'ayi. Mutane da yawa! Yau, a nan, zan iya ba ku fiye da mutane ɗari da suka ƙi tsattsauran ra'ayi saboda wa'azin da nake yi.
"Zan baku mutum sama da dubu daya. A jami'ar Abubakar Tafawa Balewa, a matsayinsu na dalibai, da yawa daga cikinsu sun bar jami'ar, amma saboda koyarwana suka dawo suka kammala karatunsu. Kuma wasu daga cikinsu yanzu injiniyoyi ne."
KU KARANTA KUMA: Hukumar Hisbah ta kama matasa mata da maza da basa azumi a jihar Kano
A baya mun ji cewa Ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani, Isa Pantami, ya ce zarge-zargen cewa yana da alaka da masu tsattsauran ra'ayi karya ce kawai.
Pantami ya fadawa jaridar Premium Times a wata hira ta musamman a ranar Juma’a, 16 ga watan Afrilu, cewa mutanen da ke adawa da yadda gwamnati ke hada lambar NIN da lambobin wayoyi sune ke yada zargin.
Ya yi ikirarin cewa wasu tawaga sun dauki aniyar dakatar da manufar yin rajistar shaidar zama dan kasa ga dukkan ‘yan Najeriya da kuma wadanda ke zaune a kasar.
Asali: Legit.ng