Matawalle ya ɗauki mataki kan Hakimin da ya bawa sojan da aka kama yana taimakon ƴan bindiga sarauta

Matawalle ya ɗauki mataki kan Hakimin da ya bawa sojan da aka kama yana taimakon ƴan bindiga sarauta

- Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya dakatar da hakimin Badarawa, Surajo Namakkah

- Gwamnan ya dauki wannan matakin ne bayan hakimin ya bawa wani soja da aka kama yana sayarwa yan bindiga makamai sarauta

- Daga yanzu, gwamnan ya haramtawa masu sarautun gargajiya nada sarauta a jihar ba tare da neman izini ba

Bello Matawalle, gwamnan jihar Zamfara ya dakatar da Surajo Namakkah, hakimin Badarawa a masarautar Shinkafi a jihar.

Yusuf Idris, direktan watsa labarai na gwamnan ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar a ranar Juma'a, The Cable ta ruwaito.

Matawalle ya dauki mataki kan Hakimin da ya bawa sojan da aka kama yana taimakon ƴan bindiga sarauta
Matawalle ya dauki mataki kan Hakimin da ya bawa sojan da aka kama yana taimakon ƴan bindiga sarauta. Hoto: @ChannelsTV
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yadda mutanen gari suka kashe 'yan bindiga 30 a Katsina

A cewar NAN, gwamnan ya dakatar da hakimin ne saboda bawa wani soja da aka kama yana sayar wa ƴan bindiga makamai sarautar Durumbu.

A baya bayan nan ne aka kama jami'in sojan da harsashi sinƙi 20 masu tsawon 63mm.

An ce yana daf da mika harsashin ga wani Kabiru Bashiru na ƙauyen Maniya ne a masarautar Shinkafi kuma har ya karbi kudi N100,000 daga hannun ƴan bindigan.

Gwamnan ya ce ba zai amince da duk wani abu da zai kawo koma baya a zaman lafiyar da aka samu a jihar ba.

Matawalle ya tabbatar wa mutanen jihar cewa za a hukunta duk wani da aka samu da hannu wurin kai hare-hare a jihar.

KU KARANTA: Komawar wasu mata biyu Musulunci ta haifar da cece-kuce

Ya kuma gargadi masu sarautun gargajiya su rika neman amincewa kafin su bawa wani sarauta don gudun abin da zai kunyata gwamnatin da masarautar gargajiya.

Gwamna ya ce abin bakin ciki ne a samu wasu jami'an tsaro na hada kai da ƴan bindiga.

"Kasar nan ba za ta samu nasarar cin galaba kan yan bindiga ba idan akwai baragurbi irinsu a hukumomin tsaro," in ji shi.

A wani labarin daban, direbobin motoccin haya da ke bin titin Gusau zuwa Dansadau a jihar Zamfara sun shiga yajin aikin sai baba ta gani saboda yawaitar fashi da makami da garkuwa da ke yawan faruwa a hanyar, Daily Trust ta ruwaito.

Titin ya kasance wayam babu motocci tun kwanaki hudu da suka gabata domin direbobin sun ki fitowa aiki.

Shugaban kungiyar direbobi na kasa reshen Dansadau, Isihu Ticha ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa sun shiga yajin aikin ne domin janyo hankalin mahukunta kan halin da suke ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel