Komawar wasu mata biyu Musulunci ta haifar da cece-kuce
- Wasu mata biyu da ke aikin kula da gida a kasar Libya sun amshi addinin musulunci
- Kafafen watsa labarai a kasar na Libya sun wallafa hotuna matan biyu bayan sun musulunta
- Masu bibiyan dandalin sada zumunta sun tafka mahawara kan batun inda wasu ke taya su murna, wasu na zargin an tilastasu ne ko kuma don neman kudi suka musulunya
Wasu mata biyu da ke aikin gida a birnin Tripoli a kasar Libya sun karbi addinin musulunci kamar yadda rahotanni suka nuna.
Wata kafar watsa labarai na kasar, The Libya Observer ta wallafa hotunan matan yan Nigeria bayan sun karbi musulunci a ranar Laraba 14 ga watan Afrilu.
DUAB WANNAN: Mutum 10 sun mutu, wasu 500 na asibiti bayan shan gurbataccen sinadari a Kano
Sai dai wannan rahoton ya janyo maganganu inda mutane suka rika bayyana mabanbantan ra'ayoyi game da musuluntar matan.
Yayin da wasu ke farin ciki cewa matan sun amshi addinin gaskiya, mafi yawancinsu yan Nigeria mazauna Libya, wasu na ikirarin cewa an tilastawa matan ne ko kuma kudi ne yasa suka musulunta.
Wani Abubakar ya ce: "Na taya su murnar shiga musulunci kuma ina kira ga wasu yan Nigeria da ke cewa an tursasa musu karbar addinin. Wannan ba abu mai kyau bane. Ba ku yi wa yan Libya adalci kuma na san abin da yasa kuke yi don yan Libya suna cutar da ku. Amma ku sani cewa musulunci bai koyar da su hakan ba. Idan kuka kalli musulmi a Nigeria ba su cutar da kirista ko wanda ba musulmi ba, wannan ya isa ku fahimta. Musulunci baya koyar da musgunawa musulmi kuma bai amince bai amince da cin zali. Ina shawartar ku idan ba ku yi wa musulunci adalci, ku dena zuwa kasarsu. Amma musulunci addini ne na adalci, ba na takura ba. Ku tafi ku yi bincike."
Yusuf Bello ya ce: "Musulunci ne addinin da ya fi bunkasa a duniya yanzu... Ina muku murna."
DUBA WANNAN: BBOG: Ƴan Nigeria sun ɗau addini a kai amma imaninsu sai a hankali, Aisha Yesufu
Enaluna Okokhuele Oboh ta rubuta: "Menene labari a cikin wannan? Tunda dama musulunci addini ne a Nigeria kuma akwai musulmai a Nigeria. Mene kuke son fada mana? Ko dai akwai lauje cikin nadi ne? Ko Baba Buhari ai dan uwanku ne musulmi."
Okoye Agubatofia ya ce: "Ku kuka san abinda kuka musu alkawari kafin suka amshi musulunci, domin nima na taba zuwa kasar, sun yi alkawarin yi min sha tara na arziki domin in musulunt amma ban yarda ba, sun ma yi alkawarin cewa za su gina min gida kuma zan auri mata yar kasarsu amma ban yarda ba."
A wani labarin daban, direbobin motoccin haya da ke bin titin Gusau zuwa Dansadau a jihar Zamfara sun shiga yajin aikin sai baba ta gani saboda yawaitar fashi da makami da garkuwa da ke yawan faruwa a hanyar, Daily Trust ta ruwaito.
Titin ya kasance wayam babu motocci tun kwanaki hudu da suka gabata domin direbobin sun ki fitowa aiki.
Shugaban kungiyar direbobi na kasa reshen Dansadau, Isihu Ticha ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa sun shiga yajin aikin ne domin janyo hankalin mahukunta kan halin da suke ciki.
Asali: Legit.ng