Yadda mutanen gari suka kashe 'yan bindiga 30 a Katsina

Yadda mutanen gari suka kashe 'yan bindiga 30 a Katsina

- Mazauna kauyen Majifa a karamar hukumar Kankara na jihar Katsina sun ce sun kashe a kalla yan bindiga 30

- Mutanen garin sun ce sun samu labarin cewa yan bindigan za su kawo musu hari cikin dare ne don haka suka shirya musu tarko suka yi nasara a kansu

- Amma rundunar yan sandan jihar Katsina ta ce babu gaskiya cikin lamarin domin DPO da tawagarsa ba su ga gawa ba a garin

Mazauna kauyen Majifa da 'yan banga a karamar hukumar Kankara sun kashe a kalla mutane 30 da ake zargin yan bindiga ne a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Duk da cewa bayanai basu kamalla fitowa ba a lokacin hada wannan rahoton, majiyar Legit.ng ta gano cewa yan kauyen sun kafa wa yan bindigan tarko ne.

Yadda mutanen gari suka kashe 'yan bindiga 30 a Katsina
Yadda mutanen gari suka kashe 'yan bindiga 30 a Katsina. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Komawar wasu mata biyu Musulunci ta haifar da cece-kuce

Wani mazaunin kauyen ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa lamarin ya faru ne da asubahin ranar Litinin.

"Mazauna kauyen sun samu labarin cewa yan bindigan na shirin kawo musu hari cikin dare, hakan yasa suka kafa musu tarko kuma Allah ya basu nasara suka fatattake su suka kashe a kalla 30 daga cikin yan bindigan," in ji shi.

Amma, ya ce wasu yan bindigan sun dawo a kan rakuma sun kwashe gawarwakin, inda ya ce, "Mutanen kauyen na jira gari ya waye kafin su kona gawarwarkin amma suka farka suka ga an kwashe gawarwakin, sannan wasu da ke kauyen da ke makwabtaka da su sun tabbatar wasu mutane sun kwashe gawarwakin a kan rakuma."

Wannan shine karo na uku a cikin makonni uku da mazauna kauyen ke yin fito na fito da yan bindigan.

A ranar Lahadi, mazauna garin Magama da karamar hukumar Jibia sun yi gaba da gaba da yan bindiga sun kashe uku daga cikinsu.

KU KARANTA: Yadda miji ya kashe babban limami bayan kama shi zigidir da matarsa a gidan maƙwabta

Amma, da aka tuntubi kakakin yan sandan jihar, SP Isah Gambo, bai iya tabbatar da afkuwar lamarin ba inda ya ce zai tuntubi DPO na kananan hukumomin.

Gambo ya ce rahoton kashe yan bindiga 30 din ba gaskiya bane domin a lokacin da DPO da tawagarsa suka tafi garin ba su tarar da koda gawa daya ba.

A wani labarin daban, direbobin motoccin haya da ke bin titin Gusau zuwa Dansadau a jihar Zamfara sun shiga yajin aikin sai baba ta gani saboda yawaitar fashi da makami da garkuwa da ke yawan faruwa a hanyar, Daily Trust ta ruwaito.

Titin ya kasance wayam babu motocci tun kwanaki hudu da suka gabata domin direbobin sun ki fitowa aiki.

Shugaban kungiyar direbobi na kasa reshen Dansadau, Isihu Ticha ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa sun shiga yajin aikin ne domin janyo hankalin mahukunta kan halin da suke ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel