APC ta yi babban rashi yayinda manyan jiga-jiganta 2 suka koma PDP tare da Magoya baya 1,000
- Jam’iyyar APC reshen jihar Delta ta gamu da babban cikas yayin da wasu manyan mambobinta suka sauya sheka zuwa PDP
- Manyan ‘yan siyasan biyu, Peres Oloye da Agodi Agbor, sun jagoranci magoya bayan su sama da 1,000 zuwa PDP
- Masu sauya shekar sun ce sun fice daga APC ne saboda mummunan halin da take nuna wa kabilar Ijaw da rikicin cikin gida mara iyaka
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta rasa dan takarar ta na majalisar wakilai a zaben 2019 a jihar Delta, Peres Oloye, zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Hakazalika, babban jagoran APC kuma sakataren yada labarai na jam'iyyar a yankin Delta ta Kudu, sanata Agodi Agbor, ya fice daga jam'iyyar zuwa PDP, jaridar Vanguard ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: 2023: Nan babu dadewa wasu gwamnonin PDP zasu dawo APC, Yahaya Bello
Legit.ng ta tattaro cewa manyan jiga-jigan yan siyasar biyu sun jagoranci magoya bayansu sama da 1,000 zuwa PDP a jihar Delta.
Mutanen biyu wadanda dukkaninsu suna PDP a baya sun samu kyakkyawan tarba a wani biki da aka gudanar a garin Tuomo da ke karamar hukumar Burutu ta jihar.
Oloye ya ce ya koma APC ne a shekarar 2018 domin kare kasar Ijaw amma daga baya sai ya gano cewa jam' iyyar na matukar adawa da Ijaw, yana mai zargin cewa babu wani dan kabilar Ijaw Delta da ake ganin ya dace da duk wani mukami.
Ya kara da cewa jam'iyyar APC a jihar tana fama da rikici da rashin hadin kai a cikin gida, don haka ya yanke shawarar komawa PDP.
A nasa bangaren, Agbor ya ce rashin iyawar APC wajen samar da dandamalin shigar da kowa a jihar Delta, adawa mara amfani, da dai sauransu, sune dalilansa na yanke shawarar komawa PDP, jaridar Nigerian Tribune ma ta ruwaito.
Oloye, Agbor da magoya bayansu sun samu tarba daga shugaban PDP a karamar hukumar Burutu, Ebike Oromoni, a madadin shugabannin jam'iyyar na jihar.
KU KARANTA KUMA: Buhari ya bayyana dalilinsa na nada Usman Alkali Baba sabon IGP
Oromooni wadanda suka nuna farin cikinsu da dawowar su biyun da mabiyansu zuwa jam'iyyar sun ce ba za a dauke su a matsayin sabbin masu zuwa ba.
A wani labarin, Nyesom Wike, gwamnan jihar Ribas, ya ce duk wanda ke neman zama shugaban kasa a 2023 zai bukaci samun kuri'u a Ribas sannan ya hada kai da Kano ko Legas don samun nasara.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa ya ce irin wannan gagarumar matsayar ce ta tabbatar da mahimmancin Ribas a cikin tsarin siyasar kasar nan, yana mai cewa babu wanda za a bari ya bata shi.
Legit.ng ta tattaro cewa Wike, a cikin wata sanarwa ta hannun mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Kelvin Ebiri, ya yi magana a babban taron karshe na yakin neman zaben kananan hukumomin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Ulakwo da ke karamar hukumar Etche a ranar Alhamis, 15 ga Afrilu.
Asali: Legit.ng