2023: Ribas ce zata tantance wanda zai gaji Buhari, Wike ya bayyana
- Gwamna Nyesom Wike ya ce babu wanda zai iya zama shugaban kasa a 2023 ba tare da kuri’un Ribas ba
- Wike ya bayyana cewa yankin kudu maso kudu ne zai tantance wanda zai gaji shugaba Buhari
- A cewarsa, PDP ta koyar da APC wani babban darasi mai daci a jihar Ribas a 2019
Nyesom Wike, gwamnan jihar Ribas, ya ce duk wanda ke neman zama shugaban kasa a 2023 zai bukaci samun kuri'u a Ribas sannan ya hada kai da Kano ko Legas don samun nasara.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa ya ce irin wannan gagarumar matsayar ce ta tabbatar da mahimmancin Ribas a cikin tsarin siyasar kasar nan, yana mai cewa babu wanda za a bari ya bata shi.
KU KARANTA KUMA: Yan matan Chibok: Gwamnati bata san mutuncin talaka ba sai lokacin neman kuri’u - Aisha Yesufu
Legit.ng ta tattaro cewa Wike, a cikin wata sanarwa ta hannun mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Kelvin Ebiri, ya yi magana a babban taron karshe na yakin neman zaben kananan hukumomin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Ulakwo da ke karamar hukumar Etche a ranar Alhamis, 15 ga Afrilu.
Ya ce:
“Ina ta fadawa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) cewa babu jihar da ta baiwa jam’iyyar kuri’u sama da Ribas.
"Kuma a Ribas ne kawai, a duk yankin kudu maso kudu, jam’iyyar All Progressives Congress (APC) bata samu kuri’u 25% a babban zaben 2019 ba. Mun koya musu darasi."
KU KARANTA KUMA: Sanatocin Najeriya 7 da ke sanya suttura ta musamman da kyawawan hotunan su
A wani labarin, gwamnan jihar Kogi kuma shugaban kwamitin tuntuba na jam'iyya mai mulki ta APC, Yahaya Bello, ya ce gwamnoni masu yawa daga jam'iyyar PDP da sauran manyan jam'iyyu na kokarin komawa APC.
Wannan na zuwa ne bayan rade-radin da ake yi na cewa gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya shirya tsaf domin barin jam'iyyar PDP zuwa APC.
Yayin zantawa da manema labarai bayan taron sirri da yayi da kwamitinsa a hedkwatar jam'iyyar APC a ranar Alhamis a Abuja, Gwamna Bello yace jam'iyyar adawa ta san abubuwan dake faruwa a APC.
Asali: Legit.ng