Buhari ya bayyana dalilinsa na nada Usman Alkali Baba sabon IGP

Buhari ya bayyana dalilinsa na nada Usman Alkali Baba sabon IGP

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace zabinsa na Baba a matsayin sabon IGP yayi shi ne saboda gogewarsa

- Buhari yace shugaban 'yan sandan yana da gogewa tare da horarwar da ake bukata domin shawo kan matsalar tsaro

- Buhari ya nada Usman Alkali Baba a matsayin sabon IGP inda ya maye gurbin tsohon sifeta janar Mohammed Adamu

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi bayanin dalilin da yasa ya zabi Alkali Baba a matsayin sabon mukaddashin sifeta janar na 'yan sandan Najeriya.

Bayan sanarwar da aka yi, mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya kawata IGP a ranar 7 ga watan Afirilu yayin da Buhari yake kasar Landan domin duba lafiyarsa.

Wannan sanarwan ta nadin sabon IGP ya janyo cece-kuce inda wasu ke ganin bai dace ba a kundin tsarin mulki.

KU KARANTA: Bidiyon sojin Najeriya suna wakokin sukar Boko Haram ya taba zukata

Buhari ya bayyana dalilinsa na nada Usman Alkali Baba sabon IGP
Buhari ya bayyana dalilinsa na nada Usman Alkali Baba sabon IGP. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Mahaifiyar amarya ta tsere da sadakin diyarta, ta bar madaura aure da Lahaula

Amma kuma, Muhammad Dingyadi, ministan al'amuran 'yan sanda, ya kare hukuncin shugaban kasan inda yace yabi doka a nadin da yayi.

A yayin jawabi ga manema labaran gidan gwamnati bayan dawowarsa kasar a ranar Alhamis, Buhari yace an bashi jerin sunayen 'yan takarar inda ya zabi Baba ganin cewa yana da gogewar da ake bukata.

"Tabbas mun duba lamarin, akwai kwamitin al'amuran 'yan sanda wanda ministan ke jagoranta. Sun bani sunaye kuma shine naga yafi cancanta," yace.

"Ya san aikin sa. Ya dade yana yi na tsawon lokaci kuma ya samu horarwa mai yawa. Yana da gogewa don haka muke tsammanin zai iya."

Kamar yadda Kamfani Dillancin Labaran Najeriya ta ce, yayi kira ga hafsoshin tsaro da su inganta harkar tsaro a kasar nan.

"Yauwa, wadannan shugabannin tsaron sun dade a harkar. Sun san mene ne matsalar. Sun san abinda ya dace kuma a tunani na suna yin abinda ya dace. Ina fatan zasu samar da abinda ake bukata ga 'yan Najeriya," yace.

A wani labari na daban, Samuel Ortom, gwamnan jihar Benue, ya ce bai sake iya runtsa bacci ba tun bayan da aka kashe sojoji 11 a jiharsa. An kashe sojojin a kauyen Bonta dake karamar hukumar Konshisha a Benue.

Gwamnan a ranar Laraba ya yi wa shugaban kasan ta'aziyya tare da rundunar sojin a kan lamarin da ya faru, The Cable ta ruwaito.

Ya yi wannan jawabin ne yayin da Bashir Magashi, ministan tsaro da kuma hafsoshin tsaro suka kai masa ziyara a Makurdi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel