2023: Nan babu dadewa wasu gwamnonin PDP zasu dawo APC, Yahaya Bello
- Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi yace wasu gwamnonin PDP na shirin komawa APC
- Gwamnan ya sanar da hakan ne a Abuja bayan taron sirri da suka yi da 'yan kwamitinsa
- Bello ya sanar da hakan ne yayin da ake rade-radin cewa Gwamna Matawalle zai sauya sheka
Gwamnan jihar Kogi kuma shugaban kwamitin tuntuba na jam'iyya mai mulki ta APC, Yahaya Bello, ya ce gwamnoni masu yawa daga jam'iyyar PDP da sauran manyan jam'iyyu na kokarin komawa APC.
Wannan na zuwa ne bayan rade-radin da ake yi na cewa gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya shirya tsaf domin barin jam'iyyar PDP zuwa APC.
Yayin zantawa da manema labarai bayan taron sirri da yayi da kwamitinsa a hedkwatar jam'iyyar APC a ranar Alhamis a Abuja, Gwamna Bello yace jam'iyyar adawa ta san abubuwan dake faruwa a APC.
KU KARANTA: Katsina: An yankewa gagarumin dilan miyagun kwayoyi hukuncin shekaru 15 a gidan yari
KU KARANTA: Bidiyon sojin Najeriya suna wakokin sukar Boko Haram ya taba zukata
"Ina da kwamitin matasa, mata da kuma masu nakasa wanda muke janyowa jam'iyyarmu.
"Kamar yadda muke janyo matasa, mata da masu nakasa, haka muke kokarin janyo 'yan wasu jam'iyyun siyasa da suka hada da gwamnoni.
“Idan zaku tuna, akwai matasa da kuma matasa a zukatansu. Hakan yasa muke kokarin kawo su cikin jam'iyyarmu. Za ku gansu da yawansu.
“Na fadi muku, akwai wani gwamna daya da zai dawo jam'iyyarmu daga karshe kuma hakan zai sa sauran su garzayo saboda nan ne komai ke faruwa na cigaban kasar nan.
"Hakan ne yasa nace muna kara karfi kuma muna samun cigaba a dunkule," yace.
A wani labari na daban, an yi wata karamar hatsaniya wurin biyan sadaki bayan an gano cewa mahaifiyar amarya tayi sama da fadi da kudin sadakin da sirikanta suka kai.
Mahaifiyar amaryar mai suna Anne Maweni, an gano cewa ta yi tsammanin iyayen amaryan zasu yi mata mugunta, lamarin da yasa ta tsere da sadakin da ya kai Sh170,000.
An fara shirin auren a Garsen, yankin Tana River dake Kenya yayin da 'yan uwa suka cewa, Maweni, mahaifiyar amaryar bata nan, The Nation ta ruwaito.
Asali: Legit.ng