Yan matan Chibok: Gwamnati bata san mutuncin talaka ba sai lokacin neman kuri’u - Aisha Yesufu
- Shugabar kungiyar BBOG, Aisha Yesufu ta caccaki gwamnatin tarayya a yayinda yan matan Chibok suka cika shekaru bakwai a hannun Boko Haram
- Aisha Yesufu ta ce sam gwamnatin Najeriya bata ganin mutuncin talakawa sai a lokacin da suke neman kuri'u a wajensu
- Ta kuma zargi gwamnatin tarayya da rashin zaunar da iyayen yaran domin yi musu magana koda ta fatar baki ce
Aisha Yesufu mai raijin fafutukar dawo da yan matan Chibok ta koka a kan kunnen uwar shegu da gwamnatin tarayya tayi da lamarin yan makarantar.
Aisha ta ce da zaran ranar 14 ga watan Afrilu yayi, sai gwamnati ta fito tayi jawabi kan yaran, inda a cewarta daga nan sai tayi watsi da lamarin sai kuma wata shekara.
A hira da Legit.ng Hausa tayi da ita, mai fafutukar ta ce ya kamata gwamnati ta dunga tattaunawa da iyayen yaran don basu baki amma bata yin haka.
KU KARANTA KUMA: Sanatocin Najeriya 7 da ke sanya suttura ta musamman da kyawawan hotunan su
Ta ci gaba da cewa babu kowani taimako da gwamnati ke yi wa iyayen koda kuwa ta maganar fatan baki ne. Hakan kuma rainin hankali ne.
Game da ko akwai wani taimako da gwamnati ke baiwa iyayen yaran, Aisha Yesufu ta ce:
"Babu abunda gwamnati ke yi masu ko waya ko a hada su a basu jawabi. Sai dai ma iyayen sukan kira mu lokaci zuwa lokaci suna tambayanmu shin dan Allah mun ji wani abu ko an fada mana wani abu mune ke Abuja.
"Abun da bakin ciki da rainin hankali, babban abun da yake za ka ga gwamnatin Najeriya idan mutane suka ga talakawa irin rainin da suke yi wa talakawa ba kadan bane, amma idan lokacin da za a yi zabe ne sun san cewa talakawa ne ke fitowa zabensu suke sa su a wajen. Amma idan lokacin da za a basu shugabanci nagari ne sai a dunga yi masu rashin mutunci.
"Na tabbata da yaran Chibok yaran masu kudi ne da babu wanda zai yi masu wannan rashin mutuncin ko magana mai dadi ne. Ba ma wai a dawo maku da yaranku ba a’a a fada maku magana ta fatan baki mai dadi ma babu."
KU KARANTA KUMA: Mahaifiyar amarya ta tsere da sadakin diyarta, ta bar madaura aure da Lahaula
A wani labarin, yayin ganawar da Fasto Enoch Adeboye yayi da Nasir El-Rufai a ranar Talata 13 ga Afrilu, ya bayyana wasu bayanan sirri game da gwamnan na Kaduna.
Ziyarar Adeboye zuwa gidan gwamnatin jihar ta zo ne a daidai lokacin da aka sako mambobin cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG), jaridar Punch ta ruwaito.
A cewar jaridar Daily Trust, a ziyarar, shahararren malamin ya bayyana cewa ya dade da sanin gwamnan, ya kara da cewa gwamnan ya kasance mutum mai kirki.
Asali: Legit.ng
Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng
Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng