Sanatocin Najeriya 7 da ke sanya suttura ta musamman da kyawawan hotunan su

Sanatocin Najeriya 7 da ke sanya suttura ta musamman da kyawawan hotunan su

Idan ana maganar iya ado, ‘yan Najeriya gwanaye ne. Ba a bar wasu yan siyasar kasar a baya ba wadanda an san su da salon ado na musamman.

Legit.ng ta shiga majalisar dattijai kuma ta zakulo muku sanatoci 7 da za ka samu sun kware a wannan fannin.

Sanatocin Najeriya 7 masu salo na musamman wajen saka sutura

1. Sanata Ibikunle Amosun

Dan majalisar mai wakiltar yankin Ogun ta tsakiya an san shi da dogon hular Yarbawa. Wannan shi ne irin salon adon da ya ke amfani da shi lokacin da yake gwamnan jihar.

Amosun ya kasance dan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ne.

Sanatocin Najeriya 7 da ke sanya suttura ta musamman da kyawawan hotunan su
Sanatocin Najeriya 7 da ke sanya suttura ta musamman da kyawawan hotunan su Hoto: Senator Ibikunle Amosun
Asali: Facebook

2. Sanata Ifeanyi Ubah

Sanata Ifeanyi Ubah shi ne dan majalisa mai wakiltar yankin Anambra ta Kudu a majalisar dattijai. Zaka samu Ubah sanye da hula mai kyalli ko hula mai malafa.

Sanatan na farko ya kasance dan jam’iyyar Young Progressive Party (YPP).

KU KARANTA KUMA: Kyaftin din Super Eagles Ahmed Musa ya kammala cibiyar wasanninsa ta miliyoyin naira a Kaduna

Sanatocin Najeriya 7 da ke sanya suttura ta musamman da kyawawan hotunan su
Sanatocin Najeriya 7 da ke sanya suttura ta musamman da kyawawan hotunan su Hoto: Senator Dr. Patrick Ifeanyi Ubah
Asali: Facebook

3. Sanata Ali Ndume

Dan majalisar da ke wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawa yana jin dadin sanya farin babban riga tare da farin hula. Ya kasance dan jam’iyyar All Progressives Congress kuma ya kasance a majalisar dattijai tun daga 2011.

Sanatocin Najeriya 7 da ke sanya suttura ta musamman da kyawawan hotunan su
Sanatocin Najeriya 7 da ke sanya suttura ta musamman da kyawawan hotunan su Hoto: Senator Mohammed Ali
Asali: Facebook

4. Sanata Opeyemi Bamidele Opeyemi

Bamidele yana wakiltar yankin Ekiti ta Tsakiya a zauren majalisar. Sanatan galibi yakan sanya farin hular sa akan kayan gargajiya. Ya kasance dan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.

Sanatocin Najeriya 7 da ke sanya suttura ta musamman da kyawawan hotunan su
Sanatocin Najeriya 7 da ke sanya suttura ta musamman da kyawawan hotunan su Hoto: Opeyemi Bamidele
Asali: Facebook

5. Sanata Ajibola Basiru

Dan majalisar da ke wakiltar yankin Osun ta Tsakiya ya kasance dan majalisar dattawa a karo na farko. Yana jin daɗin sanya tufafin gargajiya tare da gajeren wando.

KU KARANTA KUMA: Tafiyar ganin likita a Ingila: Daga ƙarshe FG ta magantu game da dawowar Shugaba Buhari

Sanatocin Najeriya 7 da ke sanya suttura ta musamman da kyawawan hotunan su
Sanatocin Najeriya 7 da ke sanya suttura ta musamman da kyawawan hotunan su Hoto: Ajibola Basiru
Asali: Facebook

6. Sanata Ajayi Boroffice

Sanata Boroffice mafi yawan lokuta yana bayyana a majalisar dattijai tare da fararen shiga ta gargajiya, farar hula da farin takalmi.

Sanatan yana wakiltar yankin Ondo ta Arewa. Ya kasance mataimakin shugaban masu rinjaye a majalisar dattijai kuma dan jam'iyyar All Progressives Congress mai mulki.

Sanatocin Najeriya 7 da ke sanya suttura ta musamman da kyawawan hotunan su
Sanatocin Najeriya 7 da ke sanya suttura ta musamman da kyawawan hotunan su Hoto: Sen Robert Ajayi Boroffice
Asali: Facebook

7. Sanata Yisa Orker-Jev

Dan majalisar da ke wakiltar yankin Benuwai ta Arewa maso yamma a majalisar yana jin dadin sanya kayan gargajiya da hula fari da baki. Shi dan jam’iyyar PDP ne.

Sanatocin Najeriya 7 da ke sanya suttura ta musamman da kyawawan hotunan su
Sanatocin Najeriya 7 da ke sanya suttura ta musamman da kyawawan hotunan su Hoto: Sen Emmanuel Yisa Orker-jev
Asali: Facebook

A wani labari, a makon nan ne kamfanin sada zumunta ta Twitter ta sanar da dasa hedkwatarta ta Afrika a kasar Ghana, lamarin da ya jawo cece-kuce a tsakanin jama'ar Najeriya.

Jam'iyyar adawa ta PDP ta caccaki gwamnatin Buhari, tare da alakanta dasa hedkwatar ta Twitter a kasar Ghana da rashin kwarewar mulkin shugaba Buhari.

PDP ba ta bar jam'iyyar APC ba, ta kuma hada da jam'iyyar mai ci ta ce akwai laifinta a cikin lamarin kai hedkwatar Twitter din Ghana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng