Bidiyon sojin Najeriya suna wakokin sukar Boko Haram ya taba zukata

Bidiyon sojin Najeriya suna wakokin sukar Boko Haram ya taba zukata

- Bidiyon wasu zakakuran sojin Najeriya suna waka tare da kushe lamarin Boko Haram ya taba zukatan jama'a

- A gajeren bidiyon, an ga sojojin tare da jinsu suna cewa 'yan ta'adda su daina amfani da sunan Allah suna kashe jama'a

- Kamar yadda sojojin suke cewa, Allah mai grima ne da buwaya kuma baya kashe jama'a don haka su dena fakewa da shi suna barna

Wasu sojin Najeriya da ke fama da yaki da 'yan ta'adda a yankin arewa maso gabas sun shirya wata waka ta sukar miyagun 'yan ta'addan.

A wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta, an ga sojojin suna waka yayin da wasu ke amshi tare da yin bidiyo.

A wakar, an ji zakakuran sojin suna kira ga 'yan ta'addan da su daina fakewa da Allah suna barna tare da nuna cewa suna yin kisa saboda Allah ne.

Allah mai girma ne da buwaya kuma baya kashe jama'a.

KU KARANTA: Angon da ya bace ranar bikinsa ya bayyana, yace gidan abokinsa ya je huce gajiya

Bidiyon sojin Najeriya suna wakokin sukar Boko Haram ya taba zukata
Bidiyon sojin Najeriya suna wakokin sukar Boko Haram ya taba zukata. Hoto daga @Thecableng
Asali: UGC

KU KARANTA: 2023: Fitattun mata 'yan siyasa 6 da ake sa ran zakarunsu zasu yi cara babu dadewa

Kamar yadda wakar take cewa:

"Ku dena amfani da Allahu Akbar wurin kashe mutane. Allah mai girma ne, baya kashe mutane. Boko Haram suna kashe mutane, Allah mai girma baya kashe jama'a."

Mayakan ta'addanci na Boko Haram sun dade suna cin karensu babu babbaka yankin arewa maso gabas ta kasar nan.

Suna kashe mutane babu laifin zaune balle na tsaye, kuma sune silar gudun hijirar jama'a masu tarin yawa daga yankin.

A wani labari na daban, wata mai rajin kare hakkin dan Adam mai suna Oluwatosin Adeniji, ta zargi Omoyele Sowore da neman tallafi da sunanta kuma ya samu ya adana.

A ranar Talata, 14 ga watan Afirilu ne ta je shafinta na Twitter inda tayi yayata ga Sowore akan yadda ya nemi tallafi da sunanta ba tare da ta sani ba.

Wani sashin wallafarta yace: "Sowore, abun takaici ne yadda kayi amfani da sunana tare da wahalar da na sha. Na je gidan yari a watan Nuwamban shekarar da ta gabata a kan EndSARS amma ka nemi tallafi da sunana ba tare da ka sanar dani ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel