Mahaifiyar amarya ta tsere da sadakin diyarta, ta bar madaura aure da Lahaula
- Mahaifiyar amaryar ta gudu da kudin sadakin diyarta a ranar daurin aure bayan komai ya kankama
- Anne Maweni, ta zargi dangin mahaifin diyarta da kokarin danne kudin sadakin har Sh170,000 don haka ta gudu
- An nemeta an rasa amma daga bisani tayi sakon kar ta kwana ta wayar 'yar uwarta cewa a cigaba da biki kawai
An yi wata karamar hatsaniya wurin biyan sadaki bayan an gano cewa mahaifiyar amarya tayi sama da fadi da kudin sadakin da sirikanta suka kai.
Mahaifiyar amaryar mai suna Anne Maweni, an gano cewa ta yi tsammanin iyayen amaryan zasu yi mata mugunta, lamarin da yasa ta tsere da sadakin da ya kai Sh170,000.
An fara shirin auren a Garsen, yankin Tana River dake Kenya yayin da 'yan uwa suka cewa, Maweni, mahaifiyar amaryar bata nan, The Nation ta ruwaito.
KU KARANTA: Ba a zabe ni domin biyan albashin ma'aikata ba, Gwamna El-Rufai
KU KARANTA: Masoya tun daga sakandare sun angwance bayan shekaru 15 suna soyayya
"Da aka fara bikin, ita ta baiwa baki da dattawa abinci amma sai bata zauna tare da su ba. babu wanda ya san lokacin da ta gudu," Veronica Meily, 'yar uwar Maweni ta sanar.
Duk kokarin samunta da aka yi a waya ya gagara saboda wayarta a kashe take.
Daga bisani Maweni ta tura sakon kar ta kwana ga kanwarta ta wata lamba inda tace ta jagoranci daurin auren da bikin. Daga nan ne dattawa da sirikan dake zaune suka gane cewa akwai wata matsala.
Daga bisani Maweni ta sanar da cewa tayi hakan ne saboda sun bar ta da 'ya'yan bayan rasuwar mahaifinsu kuma babu mataimaki, amma aure ya tashi sun zo kwasar rabonsu.
A wani labari na daban, wani ango yayi batan dabo a ranar bikinsa kuma kamar yadda yace, yayi hakan ne domin ya samu ya huta a gidan abokinsa saboda gajiyar da yayi.
Kamar yadda Daily Monitor ta ruwaito, Dr Patrick Mbusa Kabagame da Christabella Banturaki sun shirya auren a All Saints Cathedral Nakasero dake birnin Kampala a ranar Asabar, 10 ga watan Afirilu.
An shirya liyafa a otal na Silver Springs dake Kampala. Amma kuna a yammacin ranar mai cike da tarihi, Dr Kabagame yayi batan dabo kuma ya kashe wayarsa. Wannan ya tsorata jama'a kuma 'yan uwa, abokan arziki da sirikai sun fada tashin hankali.
Asali: Legit.ng