'Yan Boko Haram sun kashe mutum 10 a harin da suka kai Damasak

'Yan Boko Haram sun kashe mutum 10 a harin da suka kai Damasak

- An tabbatar da mutuwar mutane 10 sakamakon harin da Boko Haram ta kai Damasak

- Mustapha Bako Kolo, shugaban karamar hukumar Mobbar a jihar Borno ne ya bayyana hakan

- Baya ga wadanda suka riga mu gidan gaskiya, ya ce akwai wasu mutane kuma da suka jikkata

An tabbatar da rasuwar fararen hula 10 a harin da yan Boko Haram suka kai a daren ranar Talata a garin Damasak, hedkwatar karamar hukumar Mobbar na jihar Borno.

Shugaban karamar hukumar Mobbar, Mustapha Bako Kolo ne ya bayyana hakan kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

'Yan Boko Haram sun kashe mutum 10 a harin da suka kai Damasak
'Yan Boko Haram sun kashe mutum 10 a harin da suka kai Damasak. Hoto: @ChannelsTV
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yadda miji ya kashe babban limami bayan kama shi zigidir da matarsa a gidan maƙwabta

Wasu da ke zaune a sansanin yan gudun hijira da ba a tabbatar da adadinsu ba suma sun jikkata sakamakon harin a cewar Kolo.

Duk da cewa dakarun sojojin saman Nigeria da sojojin sama sun dakile harin, wasu mutane fararen hula da dama sun jikkata.

A cewar majiyoyi, yan ta'addan sun afka garin a motocci suka nufi inda sansanin sojoji ya ke a Damasak a yayin da mutane suka rika tserewa.

Harin na daren jiya a Damasak shine na biyu a cikin mako guda.

KU KARANTA: 'Yan fashin intanet sun yi wa JAMB kutse, sun sace miliyoyin naira

Yan ta'addan sun wallafa bidiyon harin da suka kai a karshen mako a Damasak inda suke kona gine-ginen Majalisar Dinkin Duniya da wuraren ajiye abinci.

Kawo yanzu da aka wallafa wannan rahoton, rundunar sojojin Nigeria bata yi tsokaci game da batun ba.

A wani labarin daban, dan majalisar tarayya, Sanata Orji Uzor Kalu ya ce ya yi imanin akwai wadanda ke yunkurin yi wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari zagon kasa.

Dan majalisar mai wakiltan Abia North a majalisar tarayya ya yi wannan furucin ne yayin wata hira da aka yi da shi a Channels TV a ranar Litinin 12 ga watan Afirilu.

Ya ce za a magance kallubalen tsaron inda aka hada kai tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi aka yi aiki tare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel