Gwamnonin Arewa sun yi wa Rundunar Sojoji ta'aziyyar kisar dakarunta 12 a Konshisha

Gwamnonin Arewa sun yi wa Rundunar Sojoji ta'aziyyar kisar dakarunta 12 a Konshisha

- Gwamnonin jihohin Arewa sun yi wa rundunar sojojin Nigeria ta'aziyyar rasuwar sojoji 12 a Konshisha

- Kungiyar ta bakin shugabanta kuma gwamnan Plateau, Simon Lalong ta yi Allah wadai da kisar da aka yi wa sojojin

- Gwamnonin sun yi alkawarin cigaba da taimakawa rundunar sojojin kuma ta shawarci ta cigaba da aikinta bisa doka

Kungiyar Gwamnonin Nigeria ta yi wa rundunar sojoji ta'aziyya bisa kisar sojoji 12 a karamar hukumar Konshisha a jihar Benue, inda ta yi Allah-wadai da kisar ta kuma ce bai kamata ya sake faruwa ba.

Gwamnonin sun ce abin da ya faru da sojojin na iya karya lagwan dakarun da ke iya kokarinsu domin samar da tsaro a kasar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnonin Arewa sun yi wa Rundunar Sojoji ta'aziyyar kisar dakarunta 12 a Konshisha
Gwamnonin Arewa sun yi wa Rundunar Sojoji ta'aziyyar kisar dakarunta 12 a Konshisha. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yadda miji ya kashe babban limami bayan kama shi zigidir da matarsa a gidan maƙwabta

Shugaban kungiyar gwamnonin kuma gwamnan jihar Plateau, Mr Simon Lalong ya kuma yi wa iyalan sojojin da aka kashe ta'aziyya.

Kungiyar ta bukaci rundunar sojojin kada ta karaya saboda harin amma ta cigaba da yin aikinta na kare 'yancin Nigeria da kuma taimakawa wurin samar da tsaro a cikin kasar musamman a wannan lokacin da kasar ke fama da kallubalen tsaro daban-daban.

KU KARANTA: Mazauna ƙauyukan da ke kan iyakoki na yi wa 'yan smogul leken asiri, Hukumar Kwastam

A yayin da ta yi alkawarin cigaba da bada gudunmawa da hadin kai da rundunar sojojin da sauran hukumomin tsaro, kungiyar gwamnonin ta yi kira ga rundunar sojojin ta cigaba da yin aikinta bisa ka'ida da takatsantsan a yayin da ta ke kokarin gano wadanda suka aikata wannan mummunan lamarin.

A wani labarin daban, dan majalisar tarayya, Sanata Orji Uzor Kalu ya ce ya yi imanin akwai wadanda ke yunkurin yi wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari zagon kasa.

Dan majalisar mai wakiltan Abia North a majalisar tarayya ya yi wannan furucin ne yayin wata hira da aka yi da shi a Channels TV a ranar Litinin 12 ga watan Afirilu.

Ya ce za a magance kallubalen tsaron inda aka hada kai tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi aka yi aiki tare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel