Mazauna ƙauyukan da ke kan iyakoki na yi wa 'yan smogul leken asiri, Hukumar Kwastam
- Hukumar kwastam ta yi ikirarin mazauna kauyukan da ke kan iyakoki na yi wa yan smogul leken asiri
- Albashir Hamisu, Kwanturolla na Zone ne ya bayyana hakan idan ya ce wannan zagon kasar na kawo cikas ga ayyukansu
- Ya gargadi masu wannan aikin su dena domin hakan na yi wa tattalin arzikin kasa illa tare da saka rayuwar mutane cikin hatasari
Albashir Hamisu, kwanturolla na Hukumar hana faskwabri na kasa, Kwastam ta Zone B ya koka kan yadda mazauna kauyukan da ke kan iyakoki ke yi wa masu smogul leken asiri, Daily Trust ta ruwaito.
A cewarsa, mafi yawancin mazauna kauyukan suka fadawa masu smogul yadda jami'an hukumar kwastam ke yin sintiri a garuruwan hakan na kawo cikas ga ayyukan jami'an.
DUBA WANNAN: Ahmed Musa ya ce zai koma buga wa ƙungiyar Kano Pillars wasa
Albashir ya gargadi mutane su kasance sun bawa gwamnatin tarayya hadin kai domin ta samu ikon sauke nauyin da ya rataya a kanta na hana shigowa da kaya marasa kyau cikin kasar.
Ya ce bai kamata a rika taimaka wa masu smogul ba domin suna yi wa tattalin arzikin Nigeria illa inda ya ce su na shigo da miyagun kwayoyi da sauran haramtattun kaya cikin kasar.
Ya yi bayanin cewa hukumar na Zone B ta yi nasarar kwace kayayyaki masu yawa da kudin harajinsu ya kai Naira miliyan 51.4.
KU KARANTA: Tsohon gwamna ya fallasa shirin zagon ƙasa da ake yi wa gwamnatin Buhari
Ya ce kayayyakin sun hada da shimkafar kasashen waje, man gyada, spageti, sabulan wanka, motocci, tufafi na gwanjo, madara, makaroni, sukari da kuskus.
"Mun kwace kaya sau 39 a cikin makonni biyu daga 22 ga watan Maris zuwa 8 ga watan Afrilun 2021 da kudin harajinsu ya kai N51,449,779.58 a jihohin Kaduna, Kano, Jigawa, Katsina, Kebbi, Zamfara, Sokoto da Kwara.
"Muna gargadin masu smogul su dena shigo da irin wannan haramtattun kayayakin cikin kasar mu," in ji shi.
A bangare guda kun ji cewa shahararren Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Muhammad Nuru Khalid, ya yi ikirarin cewar wadansu daga cikin masu fada-a-ji wanda ya hada da 'yan siyasa da Malaman addini, su ne asalin ma su daukar nauyin rashin tsaro a wasu sassa na kasar nan .
Ya yi wannan bayani ne a Abuja a yayin kaddamar da wata littafi da aka wallafa kamar yadda Vangaurd ta ruwaito.
Khalid ya yi ikirarin cewar 'yan ta'adda wanda da yawansu matasa ne su na aikata ta'addanci ga al'umma sakamakon mu'amalarsu da sanannu malamai da 'yan siyasa wadanda su ke son kasar ta kone kurmus.
Asali: Legit.ng