“Dole Matawalle ya rabu da kujerar Gwamna idan ya yarda ya sauya-sheka daga jam’iyyar PDP”

“Dole Matawalle ya rabu da kujerar Gwamna idan ya yarda ya sauya-sheka daga jam’iyyar PDP”

- Tun tuni ake rade-radin cewa Gwamnan Zamfara zai bar jam’iyyarsa ta PDP

- Suleiman Shuaibu Shinkafi ya ce Bello Matawalle ba zai iya sauya-sheka ba

- Shugaban kungiyar matasan na Concerned APC ya ce Matawalle zai bar ofis

Yayin da ake rade-radin cewa gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, zai bar jam’iyyar PDP, Dr. Suleiman Shuaibu Shinkafi ya yi fashin baki.

Shugaban kungiyar Concerned APC Youth ta Najeriya, Suleiman Shuaibu Shinkafi ya bayyana cewa gwamna Bello Matawalle ba zai iya barin PDP ba.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Dr. Suleiman Shuaibu Shinkafi ya na cewa tilas sai gwamnan ya ajiye mukaminsa idan ya na so ya shiga jam’iyyar APC.

KU KARANTA: APC za ta iya shan kashi a zaben 2023 - Shugaban PGF

Shugaban kungiyar matasan na jam’iyyar APC ya ce dalili shi ne ba mutane su ka zabi gwamnan ba, ganin kotu ta ba shi mulki duk da bai lashe zabe ba.

Suleiman Shinkafi ya yi hira da ‘yan jarida a Kaduna, inda ya ce bai dace gwamnan na Zamfara ya sauya-sheka bayan ya samu mulki a inuwar PDP ba.

Dr. Shinkafi ya ke cewa: “Ana tunzura gwamnan (na jihar Zamfara) ya shigo jam’iyyar APC saboda dalili guda; ya samu damar yin tazarce a kan kujerarsa.”

A cewar shugaban kungiyar Concerned APC Youth, gwamna Bello Matawalle ya fara shirin barin gidan gwamnati a 2023 domin Zamfara jihar APC ce.

“Dole Matawalle ya rabu da kujerar Gwamna idan ya yarda ya sauya-sheka daga jam’iyyar PDP”
Shinkafi da Matawalle Hoto: Daily Trust/Twitter
Asali: UGC

KU KARANTA: Rahotanni: Jam’iyyar PDP za ta sasanta Kwankwaso da Tambuwal

Da yake jawabi, Suleiman Shinkafi ya yi maganar siyasar kasa, ya ce tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari, ya fi dace wa da zama shugaban APC.

“Yari shi ne ‘dan jam’iyyar da ya fi dace wa da samun wannan kujera, saboda gudumuwar da ya bada, da amana da ya nuna tun da aka kafa jam’iyyar nan."

Tsohon gwamnan Zamfara, kuma tsohon shugaban kungiyar NGF, Alhaji Abdulaziz Yari ya na cikin masu harin kujerar shugaban jam’iyyar APC na kasa.

Kwanakin baya kun ji AbulAziz Yari ya yi kira ga Bello Matawalle ya guji barin jam’iyyar PDP, yace gwamnan Zamfara zai iya rasa kujerarsa idan ya shiga APC.

Abdulaziz Yari ya ce gwamnan na Zamfara zai yi asarar kujerarsa idan ya yi gangancin sauya-sheka zuwa APC saboda yanayin yadda kotu ta ba shi mulki a 2019.

Asali: Legit.ng

Online view pixel