Matar gwamnan Zamfara ta tabbatar da nadin membobin Miyetti Allah 20 a gwamnati
- Uwargidan gwamnan jihar Zamfara ta tabbatar da nadin mambobin kungiyar Miyetti Allah a gwamnatin jihar
- Uwargidan gwamnan ta yabawa Fulani da irin goyon baya da suke bayar wa cikin gaban gwamnatin jihar
- A madadin kungiyar, shugaban ta na jihar Zamfara ya nuna godiya da karamcin da aka nuna wa mambobinta
Uwargidan gwamnan jihar Zamfara, Hajiya Aisha Bello Muhammad Matawalle ta tabbatar da nadin mataimaka na musamman ga gwamna Bello Matawalle ga mambobi 20 na kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) a jihar.
Mai magana da yawun uwargidan shugaban kasar, Zainab Abdullahi, ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Talata, ChannelsTv ta ruwaito.
Da yake jawabi a madadin wadanda aka nadan, Shugaban kungiyar na jihar, Alhaji Tukur Abubakar ya yaba wa Uwargidan Gwamnan kan kokarinta na samar da canji mai ma’ana ga Fulani da sauran jama’ar gari, in ji sanarwar.
KU KARANTA: 'Yan bindiga sun bukaci a basu buhunan shinkafa a matsayin fansa a Abuja
Abubakar ya kuma nuna matukar godiyarsa ga Gwamna Bello Matawalle saboda goyon bayan da yake baiwa fulani tare da saka su cikin gwamnatinsa.
Ya ba da tabbacin cewa MACBAN za ta ci gaba da ba da cikakken goyon baya da hadin kai don samun nasarar gwamnatin Matawalle da ci gaban jihar.
Da take gabatar da wasikar nadin a Gusau a ranar Talata, Uwargidan Gwamnan ta taya wadanda aka nada murna tare da ba su tabbacin dorewar alakar aiki da kungiyar Miyetti Allah wajen bunkasa zaman lafiya da hadin kai a jihar.
Hajiya Aisha ta ce wadanda aka nada sun hada da mata da maza na kungiyar.
A cewar ta, wannan karamcin na nufin tallafawa mambobin kungiyar ne domin yaba musu kan inganta zaman lafiya a jihar.
KU KARANTA: EFCC kawai ta gayyace ni ne, ba kama ni ta yi ba Okorocha ya bayyana gaskiya
A wani labarin, Kungiyar ci gaban Fulani ta Gan Allah a Najeriya ta yi kira ga gwamnatocin tarayya da ta jihar Oyo da su tabbatar da dawo da Sarkin Fulanin Igangan, Alhaji Salihu AbdulKadir, zuwa garin Igangan da ke karamar hukumar Ibarapa ta Arewa a jihar.
Kungiyar ta GADFAN da ke zaune a Abuja, ta kuma roki gwamnatocin da su biya diyyar Sarkin Fulanin duk asarar da shi da mutanensa suka yi a lokacin da wani dan gwagwarmayar Yarbawa, Sunday Igboho, ya kai musu hari.
Ta kuma bukaci a gurfanar da Sunday Igboho da sauran wadanda ke da hannu wajen kitsa rikici kan Sarkin Fulanin na Igangan tare da lalata dukiyarsa, jaridar Punch ta ruwaito.
Asali: Legit.ng