Kungiyar Fulani ta nemi gwamnatin Buhari ta kame Sunday Igboho
- Kungiyar Fukani ta GAFDAN ta bukaci gwamnati ta sake Sarki Fulanin Igangan nan take
- Ta kuma bukaci gwamnatin da ta gaggauta kame Sunday Igboho da ya kai wa sarkin hari
- Hakazalika ta nemi a biya Sarkin Fulanin da jama'arsa diyyar dunkiyoyin da aka lalata
Kungiyar ci gaban Fulani ta Gan Allah a Najeriya ta yi kira ga gwamnatocin tarayya da ta jihar Oyo da su tabbatar da dawo da Sarkin Fulanin Igangan, Alhaji Salihu AbdulKadir, zuwa garin Igangan da ke karamar hukumar Ibarapa ta Arewa a jihar.
Kungiyar ta GADFAN da ke zaune a Abuja, ta kuma roki gwamnatocin da su biya diyyar Sarkin Fulanin duk asarar da shi da mutanensa suka yi a lokacin da wani dan gwagwarmayar Yarbawa, Sunday Igboho, ya kai musu hari.
Ta kuma bukaci a gurfanar da Sunday Igboho da sauran wadanda ke da hannu wajen kitsa rikici kan Sarkin Fulanin na Igangan tare da lalata dukiyarsa, jaridar Punch ta ruwaito.
KU KARANTA: Magance tsaro: An kammala horar da 'yan sandan jiha 704 na jihar Kano
Kungiyar ta bayyana wadannan bukatun ne a cikin wata sanarwa bayan da jami’anta suka kai ziyarar hadin kai ga Alhaji Salihu a Ilorin, jihar Kwara.
Sanarwar ta samu sa hannun Shugaban kungiyar na kasa da kuma Sakataren kungiyar GADFAN, Alhaji Sulaiman Yakubu da Ibrahim Abdullahi.
Sanarwar ta ce,
“Abin da ya ba mu mamaki da takaici, har zuwa wannan lokacin, Sunday Igboho yana ci gaba da walwala kamar babu abin da ya faru.
“Don haka, GADFAN, na kira ga gwamnatocin tarayya da na jihar Oyo da su tabbatar an yi wa Alhaji Salihu AbdulKadir da jama’arsa adalci ta yadda ba wai kawai tabbatar da cewa an kama Igboho da yaransa an gurfanar da su ba, a kuma biya Sarkin Fulanin da mutanensa diyya kuma su koma gidajensu.
“Harin ya kai ga konewa da lalata duka gidajensa (Sarkin Fulanin Igangan), kayayyakin gida da dabbobinsa wadanda suka hada da shanu, tumaki, awaki, turkoki, makaranta, shaguna da masallaci; da suka haura N500m.”
Ta sha alwashin lalubo duk wata hanya ta zaman lafiya da doka don tabbatar da cewa an yi adalci ga dukkan bangarorin, inda ta kara da cewa,
“Tuni mun fara tattaunawa da lauyoyinmu kuma nan ba da dadewa ba za mu dauki dukkan matakan da suka dace na shari’a idan har hukumomin da abin ya shafa ba su magance matsalar ba.”
KU KARANTA: Nasara daga Allah: ‘Yan sanda sun ceto mutane 15 da aka sace a jihar Kaduna
A wani labarin, Mataimakin ko'odinetan al'ummar Hausawa a jihar Imo, Sulaiman Ibrahim Sulaiman, wanda aka fi sani da Garkuwan Hausawa, ya yi magana a wata hira da jaridar Punch game da kisan wasu mahauta bakwai a jihar da wasu 'yan bindiga suka yi.
Sulaiman ya bayyana cewa, babu shakka kisan Hausawan bakwai wani yunkuri ne na ta da zaune tsaye, musamman ma fada ta kabilanci, yana mai nuna takaicin irin wannan aika-aikata tare da mika wuya ga kaddarar Allah.
Da aka tambayeshi dangane da abinda ya fahimta a matsayin dalilin da yasa 'yan bindigan suka kashe mahautan, Sulaiman ya ce: "Kashe-kashen na da nasaba da siyasa. Ba shi da wata alaka da 'Yan asalin Biafra ko kungiyar tsaro ta Gabas.
Asali: Legit.ng