EFCC kawai ta gayyace ni ne, ba kama ni ta yi ba Okorocha ya bayyana gaskiya

EFCC kawai ta gayyace ni ne, ba kama ni ta yi ba Okorocha ya bayyana gaskiya

- Biyo bayan rahotonnin dake yawo cewa Rochas Okorocha ya shiga hannun EFCC, ya bayyana gaskiyar lamarin

- Okorocha ya ce ba kama shi aka yi ba, kawai dai an gayyace shi ne zuwa hukumar ta EFCC

- Mataimakinsa a fannin yada labarai ya ce EFCC ba mayanka bane, don haka babu wata fargaba

Tsohon Gwamnan Imo Sanata Rochas Okorocha ya fasa kwai game da kamun da Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arziki Tu'annati (EFCC) ta yi masa bisa zargin karkatar da kudaden jama'a, The Nation ta ruwaito.

Jami'an EFCC sun kama Okorocha da misalin karfe 4:10 na yammacin ranar Talata a ofishinsa na Unity House da ke Garki, Abuja.

Amma da yake magana ta bakin mai taimaka masa ta fuskar yada labarai, Sam Onwuemeodo, Okorocha ya ce tunda hukumar yaki da cin hanci da rashawa tana aikinta ne kawai zai ba ta cikakken hadin kai.

“A gare mu, Hukumar na yin aikinta kuma ya kamata a ba ta hadin kan da take bukata. Kuma kasancewar Okorocha dan kasa ne mai bin doka, ko yaushe zai ba da hadin kai ga Hukumar kan lamuran da ke Kotuna.

KU KARANTA: Ban mutu ba, dogon suma na yi saboda tsananin rashin lafiya, in ji Ummi Zee-Zee

EFCC kawai ta gayyace ni ne, ba kame ni aka yi ba Okorocha ya bayyana gaskiya
EFCC kawai ta gayyace ni ne, ba kame ni aka yi ba Okorocha ya bayyana gaskiya Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Onwuemeodo ya ce "EFCC ba mayanka ba ne, sai dai hukuma ce da ke da matukar alhaki kuma ya kamata a gan ta haka."

Ya ci gaba da cewa ana binciken Sanatan na Imo ta Yamma ne saboda sabon shugabanci a hukumar.

A cewarsa: “Maganar gaskiya ita ce, Okorocha ya bar matsayin gwamnan jihar Imo a ranar 28 ga Mayu, 2019. Kuma jim kadan da barin sa Gwamna, Gwamnatin Imo ta rubuta koke kan koke-koke a kan sa.

“EFCC ta binciki koke-koken kuma sun kasance a Kotuna daban-daban na kasar tare da Okorocha, daliin haka.

“Kuma idan har EFCC ta yanke shawarar gayyatar Okorocha don karin bayani game da al’amuran da suka rigaya a Kotuna, musamman tare da sabon Shugaban da ke jagorantar al’amuran a Hukumar, babu wani laifi a cikin hakan.

“Abubuwan da ke tsakanin EFCC da Okorocha game da gwamnansa a Imo, sun kasance a Kotuna daban-daban na kasar.

"A karshe dai, za mu san ko Hukumar za ta janye kararrakin a Kotuna, ko za ta ci gaba da shari'ar da ta riga ta kasance a Kotuna."

KU KARANTA: JAMB ta zargi UniAbuja da ba da guraben shiga jami'a ba bisa ka'ida ba

Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya shiga hannun hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, jaridar Premium Times ta tabbatar.

Jami'an hukumar EFCC sun kama Okorocha wurin karfe 4 na yammacin Talata a ofishinsa dake Abuja, majiya ta tabbatar.

Majiyar da ta tabbatar, ta ce hukumar ta dinga tura gayyata ga tsohon gwamnan zuwa ofishinta dake Abuja saboda harkallar wasu kudade amma ya ki zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel