Wani dan majalisar dokokin jihar Nasarawa ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

Wani dan majalisar dokokin jihar Nasarawa ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

- Jam'iyyar All Progressive Congress (APC) ta yi babban kamu na dan majalisa mai wakiltar mazabar Akwanga ta kudu a majalisar dokokin jihar Nasarawa

- Mista Samuel Tsebe dai ya sauya sheka ne daga jam'iyyarsa ta Peoples Democratic Party (PDP)

- Kakakin majalisar, Ibrahim Abdullahi ne ya bayyana hakan a zaman majalisar na yau Talata

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Akwanga ta kudu a majalisar dokokin jihar Nasarawa karkashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Mista Samuel Tsebe ya sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressive Congress (APC).

Kakakin majalisar, Ibrahim Abdullahi ne ya bayyana hakan a zaman majalisar na ranar Talata, 13 ga watan Afrilu.

Ya ce ya sami wasika kan haka daga Tsebe, jaridar The Nation ta ruwaito.

Wani dan majalisar dokokin jihar Nasarawa ya sauya sheka daga PDP zuwa APC
Wani dan majalisar dokokin jihar Nasarawa ya sauya sheka daga PDP zuwa APC Hoto: techforest.ng
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Hoton wasu yan gida daya su 6 kuma dukkansu likitoci ne

Yayin taya dan majalisar da ya sauya sheka murna, kakakin majalisar ya bukace shi da ya ci gaba da mai da hankali wajen bayar da gudummawarsa domin cigaban jam'iyyar, jihar da ma kasa baki daya.

“Ina so in bayyana muku cewa na karbi takardar sauya sheka na Hon Samuel Tsebe na mazabar Akwanga ta Kudu daga PDP zuwa APC.

“Wannan wani sabon ci gaba ne a APC. An yi masa maraba sosai a cikin babbar jam'iyyarmu ta APC.

Kakakin ya ce "A madadin shugabancin majalisar, ina taya Hon Tsebe murnar sauya sheka zuwa APC, ina son tabbatar masa da samun dama daidai da kowa a cikin jam'iyyar."

KU KARANTA KUMA: Muhimman abubuwa 4 da ya kamata a sani game da ‘yan siyasa a Najeriya

A wani labarin kuma, a yayin da babban zaben shekarar 2023 ke karatowa, mutanen garin Abuja sun farka sunyi karo da hotunan tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki na neman takarar shugabancin kasa a 2023.

An lika hotunan a wasu wurarre masu daukan hankali a birnin na Abuja kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Hotunan na dauke da rubutu da ke cewa "Reset Nigeria 2023", da kuma cewa a zabi Saraki a matsayin shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel