2023: Hotunan Neman Takarar Shugaban Ƙasa na Saraki Sun Mamaye Abuja

2023: Hotunan Neman Takarar Shugaban Ƙasa na Saraki Sun Mamaye Abuja

- An wayi gari da ganin fastocin takarar Bukola Saraki sun mamaye garin Abuja, babban birnin tarayya

- An yi rubutun wasu sakonni a jikin fastocin takarar Saraki da suke neman ya ceci Najeriya a 2023 a jikin fastocin

- Sai dai Sarakin, ta bakin kakakinsa, Yusuph Olaniyonu, ya nisanta kansa da hotunan ya kuma ce idan lokaci ya yi ba a boye za su fitar da nasu ba

A yayin da babban zaben shekarar 2023 ke karatowa, mutanen garin Abuja sun farka sunyi karo da hotunan tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki na neman takarar shugabancin kasa a 2023.

An lika hotunan a wasu wurarre masu daukan hankali a birnin na Abuja kamar yadda The Nation ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Ahmed Musa ya ce zai koma buga wa ƙungiyar Kano Pillars wasa

2023: Hotunan Neman Takarar Shugaban Ƙasa na Saraki Sun Mamaye Abuja
2023: Hotunan Neman Takarar Shugaban Ƙasa na Saraki Sun Mamaye Abuja. Hoto: TheNationNews
Asali: Twitter

Hotunan na dauke da rubutu da ke cewa "Reset Nigeria 2023", da kuma cewa a zabi Saraki a matsayin shugaban kasa.

Akwai tambarin babban jam'iyyar hamayya ta Peoples Democratic Party (PDP) a jikin fastocin baya ga hoton na Saraki.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Arapaja ya zama sabon shugaban PDP na Kudu maso Yamma

Sai dai Sarakin ta bakin kakakinsa, Yusuph Olaniyonu, ya nisanta kansa da hotunan inda ya ce ba shi ya wallafa su ba kuma bai umurci wani ya masa fosta a madadinsa ba.

A hirar tarho da ya yi da wakilin majiyar Legit.ng a ranar Talata, Olaniyonu ya ce, "Ba mu san komai game da fastocin da ka ke magana a kai ba. Sai dai idan kai ne (wakilin majiyar Legit.ng) ne ka wallafa su.

"Idan lokaci ya yi da Dr Saraki zai wallafa fastoci, ba cikin sirri zai yi ba. Ba za mu boye mu wallafa fostoci ba don haka kai ya kamata mu tambaya wanene ya yi fastocin."

A bangare guda kun ji cewa shahararren Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Muhammad Nuru Khalid, ya yi ikirarin cewar wadansu daga cikin masu fada-a-ji wanda ya hada da 'yan siyasa da Malaman addini, su ne asalin ma su daukar nauyin rashin tsaro a wasu sassa na kasar nan .

Ya yi wannan bayani ne a Abuja a yayin kaddamar da wata littafi da aka wallafa kamar yadda Vangaurd ta ruwaito.

Khalid ya yi ikirarin cewar 'yan ta'adda wanda da yawansu matasa ne su na aikata ta'addanci ga al'umma sakamakon mu'amalarsu da sanannu malamai da 'yan siyasa wadanda su ke son kasar ta kone kurmus.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel