Hoton wasu yan gida daya su 6 kuma dukkansu likitoci ne

Hoton wasu yan gida daya su 6 kuma dukkansu likitoci ne

- Wata budurwa ta dora hoton 'yan uwanta a shafin sada zumunta wadanda dukkansu likitoci ne

- Ta ce ko shakka babu yan uwanta za ta zaba a kan Kardashians idan har aka bata zabi

- Masu amfani da shafin soshiyal midiya sun nuna mamaki kan haka inda suka nuna sha’awarsu a kan iyalan

Ba kowane lokaci bane ake samun yan uwan juna da ke daukar sana'a ɗaya. A yanayin da hakan ya faru, yawanci a kan samu mutum biyu, uku ko biyar ne amma iyalan Okpaleke sun banbanta.

A wani wallafa da tayi a shafin sada zumunta, wata ‘yar gidan ta buga wani hoto da ke dauke da dukkan ‘yan uwanta biyar kuma ta bayyana cewa dukkansu likitoci ne.

KU KARANTA KUMA: Muhimman abubuwa 4 da ya kamata a sani game da ‘yan siyasa a Najeriya

Hotunan wasu yan gida daya su 6 kuma dukkansu likitoci ne
Hotunan wasu yan gida daya su 6 kuma dukkansu likitoci ne Hoto: Linkedln/Chinyere Okpaleke
Asali: UGC

Matashiyar budurwar Chinyere Okpaleke wacce ita kanta likita ce ta rubuta a wani adireshin LinkedIn cewa za ta zabi iyalanta a kan fitacciyar jaruma Kardashians idan aka bata zabi.

Chinyere ta ci gaba da bayyana karfin gwiwarta a kan 'yan uwanta kuma cewa tana da tabbacin za su sanya iyayensu da kakanninsu alfahari.

A cikin hoton, dukkansu mata ne sai namiji guda daya.

Wani bangare na sakon nata ya ce:

"Na san iyayenmu da kakanninmu suna alfahari! Mun kasance daidai da manufar sadaukarwar su!"

KU KARANTA KUMA: Yanzun nan: Shugaba Buhari ya yi wani nadi mai muhimmanci

Yayinda mabiya shafin LinkedIn da dama suka cika da mamakin jin cewa yan uwa shida sun zabi sana’a daya, wasu sun jinjina masu.

Eric Singman ya yi martani:

"Kyakkyawan iyali da aka sadaukar domin yi wa dan adama hidima. Shakka babu akwai horo mai kyau daga iyaye, tabbas kuma a bayyane yake akwai kamanni mai karfi ta bangaren halitta. Ina da tabbacin cewa akwai kalubale da dama a hanyar cimma wannan kyawawan nasarori. Ina farin ciki da cewa suna da imani, soyayya, jagoranci da kuma damarmaki don cimma manufar su."

Onyeka Olisemeka ya ce:

"Abun sha’awa!!! Na so wannan. Fatan alkhairi Okpalekes!!!"

Geoffrey Nwosu ya rubuta:

"Kai. Muna godiya ga Allah bisa shiriyar da ya yi wa wannan iyalin. Amin."

A wani labarin, Ahmed Musa, kyaftin na kungiyar kwallon kafa na Nigeria, Super Eagles ya ce yana duba yiwuwar komawa kungiyar Kano Pillars na kankanin lokaci, The Cable ta ruwaito.

Tsohon mai bugawa CSKA Moscow gaba baya tare da kowanne kungiya tun bayan rabuwarsa da Al Nassr a watan Oktoban 2020.

A hirar da ya yi da BBC Sports Africa, Musa ya ce ya yi magana da Abdullahi Ganduje, gwamnan jihar Kano da Shehu Dikko, shugaban kamfanin kula da League, LMC kan yiwuwar bugawa Yaran Masu Gida wasanni kadan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng