Muhimman abubuwa 4 da ya kamata a sani game da ‘yan siyasa a Najeriya

Muhimman abubuwa 4 da ya kamata a sani game da ‘yan siyasa a Najeriya

Babu shakka, galibi 'yan siyasa a duniya suna da kamanceceniya da yawa. Amma waɗanda suke Najeriya suna da halayya da aka saba da su waɗanda galibi suna ɓata ran yawancin ƙasar.

A cikin wannan rahoton, Legit.ng ta yi la’akari da abubuwa biyar da ya kamata ku sani game da wadannan ‘yan siyasa da ke bata lamuran siyasar kasar nan.

1. Son ayyukan kyal-kyal banza, aikin ganin ido da kuma son mawakan da ke yabonsu

Ba tare da boye-boye ba, 'yan siyasa a cikin wannan yanayin suna son mawaƙan da ke yabon su. Suna son mutane waɗanda koyaushe zasu gaya musu abin da suke so su ji.

Ba wai wannan kawai ba, 'yan siyasar Najeriya galibi suna son ayyukan da zai iya zama mai kyau a ido amma ba tare da karko ba.

KU KARANTA KUMA: Yanzun nan: Shugaba Buhari ya yi wani nadi mai muhimmanci

2. Fadin komai domin su ci zabe

A lokacin zabe, komai yana tafiya. Wannan take ne a tsakanin 'yan siyasar Najeriya. Sun yi imanin cewa lokacin zaben ya ba su lasisin yin alkawurran da suka san ba za su cika ba.

Yin alkawuran da ba za su cika ba abun farin ciki ne a tsakanin su tunda sun san cewa babu wanda zai tuhume su.

Muhimman abubuwa 4 da ya kamata a sani game da ‘yan siyasa a Najeriya
Muhimman abubuwa 4 da ya kamata a sani game da ‘yan siyasa a Najeriya Hoto: Bola Alao
Asali: Twitter

3. Saurin manta alkawura

Baya ga yin alkawuran karya waɗanda ba su da niyyar cikawa, 'yan siyasa a Najeriya suna da ƙwarewa wajen manta alkawuran da suka yi, har ma da waɗanda za a iya cika su cikin sauƙi.

KU KARANTA KUMA: Ka gyara titunan da suka hada manyan kananan hukumomi a Borno, Sojojin Najeriya sun roki Zulum

4. Basu da abokai na dindindin

An ce babu aboki na dindindin a siyasa. Amma lamarin ‘yan siyasan Najeriya yana wani mataki. Za a iya zaban gwamnoni da mataimakansu a matsayin manyan abokai, kafin su bar mulki, sai su zama abokan gaba.

A zahiri, ɗan siyasa na iya yabon wani yau kuma a cikin wata ɗaya, ya kira shi kowane irin suna a cikin jama'a.

A wani labarin, mun ji cewa a yayin da babban zaben shekarar 2023 ke karatowa, mutanen garin Abuja sun farka sunyi karo da hotunan tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki na neman takarar shugabancin kasa a 2023.

An lika hotunan a wasu wurarre masu daukan hankali a birnin na Abuja kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Hotunan na dauke da rubutu da ke cewa "Reset Nigeria 2023", da kuma cewa a zabi Saraki a matsayin shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel